Yan ta'adda
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar dakile wasu hare-haren da 'yan ta'addan ISWAP suka kai a jihar Borno. Sojojin sun yi ragargaji 'yan ta'addan.
A wannan rahoto na musamman, za mu yi duba kan manyan ‘yan bindigan da aka kama ko aka kashe a farkon 2025 da yadda hakan ya shafi matsalar tsaron Arewa.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan wani yunkurin kai harin ta'addanci da 'yan ta'addan Boko Haram suka yi a jihar Adamawa. Sun fatattake su zuwa daji.
Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa dakarun tsaro sun ƙara ƙaimi wajen farautar shugaban ƴan bindiga Kachalla Dan Mai Kinni, bayan cafke yaronsa, Lawali Malangaro.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Sojojin 'Operation Fansan Yanma' sun kashe 'yan ta'adda 12 a kauyen Maigora, Faskari, suka kwato babura da dama daga hannunsu.
Sabon rahoto ya nuna cewa tsohon shugaban kasar Nijar, Ibrahim Baré Maïnassara ne ya kafa rundunar Lakurawa a 1997 domin yaki da masu satar shanu.
Rundunar 'yan sandan kasar nan ta yi nasarar hallaka matashin dan ta'adda, Dogo Saleh, wanda aka hakikance ya jawo asarar rayukan jama'a da dama bayan garkuwa da su.
Rundunar tsaro ta dakile harin ramuwar gayya na ‘yan bindiga a Mada, karamar hukumar Gusau, jihar Zamfara inda ta yi nasarar hallaka hatsabibin dan ta'adda.
Wani abin fashewa da ake zargin nakiya ne ya tashi a Borno, inda ya raunata ‘yan sanda uku, yayin da ‘yan bindiga suka kashe yara shida da ke kiwo a jihar Kogi.
Yan ta'adda
Samu kari