Yan ta'adda
'Yan bindiga sun kai hari unguwar Grow Himes da ke Chikakore a Kubwa da ke birnin tarayya Abuja. Sun yi artabu da 'yan sanda kuma sun sace mutane da dama.
Mun sami rahoto cewa jami’an tsaron a sun kama dagacin Guiwa da wasu mutum 13 bisa zargin taimaka wa ‘yan bindiga a karamar hukumar Mashegu a Niger.
Rahoton da muka samu ya tabbatar da cewa yan bindiga sun kai hari cikin masallaci a Unguwar Galadunci da ke karamar hukumar Anka a jihar Zamfara.
Yayin da jihar Katsina ke fama da hare-haren yan bindiga, Sarkin Daura Alhaji Faruq Umar-Faruq ya bayyana abin da ya fi ta’addanci muni saboda illa ga muhalli.
Babban hafsan sojojin kasa , Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya umarci sojoji da su yi mai yiwuwa wajen kawo karshen 'yan ta'adda ba tare da nuna musu tausayi ba.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan 'yan ta'addan ISWAP/Boko Haram a jihar Borno. Sojojin sun hallaka 'yan ta'adda masu yawa bayan an yi dauki ba dadi.
A wannan labarin, za a ji cewa Amnesty Int’l ta soki shirin mika Hamdiyya Sharif ga ‘yan sanda, tana cewa tana bukatar kulawar likita, ba tsangwama daga gwamnati ba.
Dakarun sojin Najeriya sun farmaki dan bindiga Kachalla Murtala a jihar Katsina. An ceto wata matar da ta shafe kwana 70 a dajin wajen 'yan bindiga masu garkuwa.
Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu ya ce an kashe 'yan ta'adda da masu laifi 13,500 tun bayan zuwan Bola Tinubu mulki a shekara 2 da suka wuce.
Yan ta'adda
Samu kari