Yan ta'adda
Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno yayi shatar jirgin sama kacokan domin a kai Soja mara lafiya Abuja ganin likita. Yayi masa rakiya da kansa har Abuja.
Mayakan ta’addancin Boko Haram sama da 49 ne suka mika wuya ga dakarun sojin Najeriya dake Damboa a jihar Borno. Ciki akwai kwamandojinsu 2, Baa Usman da Ari.
Labarin da muke samu ya bayyana cewa, an samu nasarar yin kaca-kaca da gidan wani dan ta'addan da ke samarwa su Bello Turji makamai a Arewa masu Yammacin kasa.
Rudunar sojin kasan Najeriya sun yi nasarar damke wasu jami’an CJTF dake kai wa Boko Haram bayanan sirri da kayan aiki a jihar Borno dake arewa maso gabas.
Kwamandan ‘yan bindiga Dankarami ya kwashe Mutum 44 bayan yaransa sun shiga gida-gida a Kanwa dake Zurmi. Moriki na hada N20m ta kariya da Turji ya bukata.
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina tayi ram da dagacin kauye mai suna Surajo Madawaki kan zargin hada kai da ‘yan bindiga wurin kashe Yahaya Danbai, manomi.
Gogarman ‘dan bindiga da ya shahara wurin satar shanu da dillancin miyagun kwayoyi a jihar Kaduna,Kachalla Gudau da na gaban goshinsa Rigimamme sun arce lahira.
Dakarun sojojin Najeriya na Operation Hadin Kai sun yi nasarar halaka babban kwamandan Boko Haram mai suna Abu Hassan da wasu mayakansa guda 13 a Mafa, Borno.
Rundunar sojoji ta bayyana gagarumin nasarar da dakarunta na Operation Hadarin Daji suka samu wanda ya kai ga halaka wasu kasurguman yan bindiga uku a Zamfara.
Yan ta'adda
Samu kari