Da duminsa: Gwamna ya dakatar da Sarkin da ya ba shaharren shugaban 'yan bindiga sarauta

Da duminsa: Gwamna ya dakatar da Sarkin da ya ba shaharren shugaban 'yan bindiga sarauta

  • Gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Bello Muhammad Matawalle, ya dakatar da sabon Sarkin 'Yandoto dake jihar
  • Gwamnan ya fara da nisanta kansa da yadda sarkin ya nada kasurgumin shugaban 'yan bindiga sarauta a jihar
  • Matawalle ya bukaci hakimin 'Yandoto da ya karba sarautar yayin da zai nada kwamiti domin tuhumar sabon Sarkin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta dakatar da sabon Sarkin Birnin Yandoto na karamar hukumar Tsafe ta jihar, Aliyu Garba Marafa, bayan ya yi wa fitaccen kasurgumin shugaban 'yan bindiga, Adamu Aliero sarautar Sarkin Fulani.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, wannan na kunshe ne a takardar da sakataren gwamnatin jihar, Kabiru Balarabe ya fitar kuma ya bai wa manema labarai a daren Lahadi.

Bello Matawalle
Da duminsa: Gwamna ya dakatar da Sarkin da ya ba shaharren 'dan bindiga sarauta. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Kamar yadda takardar tace,

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Zamfara: Matawalle Ya Dakatar Da Sarkin Da Ya Nada Gogarmar Dan Bindiga Sarautar Sarkin Fulani

"Ana sanar da jama'a cewa gwamnatin jihar Zamfara ta baranta kanta daga zagin nadin sarautar Sarkin Fulani wanda Sarkin Birnin 'Yandoton na karamar hukumar Tsafe yayi."
"A saboda haka, mai girma gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya yi umarni da dakatar da Sarkin a take.
"Kamar yadda ya dace, gwamnan ya amince da nada kwamiti domin bincikar lamarin da yasa Sarkin yayi wannan aikin.
“A halin yanzu, Alhaji Mahe Garba Marafa, wanda shi ne hakimin 'Yandoto zai cigaba da aiwatar da lamurran sarautar a masarautar."

Legit.ng ta zanta da Malam Aliyu, malamin makarantar sakandare a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara kan wannan cigaban.

Yace a gaskiya hyankulansu sun tashi bayan nadin sarautar da aka yi, amma labarin dakatar da basaraken da suka samu a yau Litinin ya kwantar musu da hankali.

"Mun san da shagalin nadin sarautar kuma manyan 'yan bindiga da ke addabar al'umma sun samu halarta. Al'amarin ya matukar tada mana da hankali, amma jin labarin dakatarwan da mai girma gwamna yayi wa basaraken ya kwantar mana da hankali.

Kara karanta wannan

Da walakin: 'Yan bindiga sama da 100 ne suka halarci taron nada shugabansu sarauta a Zamfara

"Ta yaya sanannen shugaban 'yan ta'adda da gwamnati ke nema ido rufe zai zamo abun ba sarauta a garin nan? Wannan ai cin zarafi ne da cin fuska ga wadanda yayi sanadin rayukan 'yan uwansu tare da wadanda ayyukan ta'addancinsa ya shafa," yace.

Hotuna: Yadda aka yi bikin naɗin sarautar riƙaƙen ɗan ta'addan da FG ke nema ido rufe

A wani labari na daban, an yi wa rikakken dan ta'adda Ado Aleru, nadin sarautar Sarkin Fulani a masarautar 'Yandoton daji dake jihar Zamfara.

'Yandoton daji tana daya daga cikin sabbin masarautu biyun da gwamnatin jihar Zamfara ta kirkiro a watan Mayun da ya gabata.

An kirkiro ta ne daga masarautar Tsafe. Sabon sarkin Yandoton Daji shine Aliyu Marafa.

Hukuncin bai wa shugaban 'yan bindigan sarauta ya biyo baya ne sakamakon kokarin da yayi na tabbatar da zaman lafiya tare da jagorantar yarjejeniya tsakanin masarautar da 'yan ta'addan da suka addabi karamar hukumar Tsafe.

Kara karanta wannan

Hotuna: Yadda aka yi bikin naɗin sarautar riƙaƙen ɗan ta'addan da FG ke nema ido rufe

Asali: Legit.ng

Online view pixel