Asiri ya Tonu: An kama jami'an tsaro suna waya da yan ta'adda bayan harin Kuje

Asiri ya Tonu: An kama jami'an tsaro suna waya da yan ta'adda bayan harin Kuje

  • Wata majiya ta bayyana cewa ana tsare da wasu yan sanda biyu bayan sun yi waya da yan ta'addan da suka tsere daga Gidan Yarin Kuje
  • Bayanai sun nuna cewa yanzu haka ana cigaba da matsar yan sandan domin gano iya matakin haɗa kan da suka bayar
  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yayin ziyarar da ya kai wurin, ya ce sashin tattara bayanan sirri sun ba shi kunya

Abuja - Yanzu haka ana tsare da jami'an hukumar yan sanda biyu kan mummunan harin da yan ta'adda suka kai gida gyaran Halin Kuje a Abuja.

Daily Trust ta ruwaito cewa yan ta'adda, waɗan da suka ci ƙarfin jami'an tsaron gidan Yarin, sun kwance Fursunoni 800, ciki har da baki ɗaya mayaƙan Boko Haram da ke tsare.

Harin gidan yarin Kuje.
Asiri ya Tonu: An kama jami'an tsaro suna waya da yan ta'adda bayan harin Kuje Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Harin wanda aka kai rana ɗaya da wani farmaki da yan bindiga suka kai wa ayarin motocin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a Katsina, ya kaɗa hanjin yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Katsina: Bayan kai wa Ayarin Buhari hari, Jirgin yaƙin NAF ya yi wa yan bindiga ruwan bama-bamai, rayuka sun salwanta

Rahoto ya nuna cewa an yi ram da yan sandan guda biyu ne bayan sun tattauna da wasu daga cikin yan ta'addan da suka tsere ta wayar Salula.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wata majiya ta shaida wa jaridar cewa:

"Biyu daga cikin 'yan ta'addan da suka tsere daga gidan Yarin sun kira jami'in ɗan sanda mai bincike, (IPO) a ɗaya daga cikin Caji Ofis ɗin mu, kuma ya masa magana mai rikitarwa."
"A yanzun dai ana cigaba da bincikar su domin gano matakin haɗin kan da ka iya yuwu wa sun bayar."

Kun bani kunya - Buhari

Yayin da ya ziyarci wurin ranar Laraba, shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya nuna damuwarsa da sashin tattara bayanan sirri, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

"Sashin tattara bayanan sirri sun bani kunya. Ta ya yan ta'adda zasu shirya, su samu makamai, su farmaki wurin da ya kafu da tsaro kuma su ci bulus? Ta ya dakarun tsaron gidan suka gaza kare harin?"

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan ISWAP sun fitar da bidiyo, sun ce su suka kai farmaki magarkamar Kuje

"Fursunoni nawa ne ake ajiye da su a gidan Yarin? Mutum nawa gidan Yarin ke ɗauka? Jami'ai nawa ne ke kan aiki lokacin? Nawa ne daga ciki suka shirya da makamai? Ina masu gadi da masu sa ido? Me suka yi? Shin Kamarar CCTV tana aiki?

- Buhari ya jefa waɗan nan tambayoyin ga jami'ai.

Awanni kaɗan bayan shugaba Buhari ya bar wurin, ƙungiyar ISWAP da ta ɓalle daga Boko Haram ta yi ikirarin ita ta ɗauki nauyin kai harin.

A wani labarin na daban kuma Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun hutu na babbar Sallah 2022

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Litinin da Talata, 11 da 12 ga watan Yuli, 2022 a matsayin na hutun shagalim babbar Sallah.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya taya ɗaukacin Musulman Najeriya murnar zagayowar wannan rana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel