Fashin magarkamar Kuje: FG ta fitar da bayanan 'yan Boko Haram din da suka tsere

Fashin magarkamar Kuje: FG ta fitar da bayanan 'yan Boko Haram din da suka tsere

  • Rahoto ya bayyana cewa, an bayyana sunayen mutanen da ake zargin 'yan Boko Haram ne kuma sun tsere daga magarkama
  • A makon nan ne aka samu hargitsi yayin da wasu 'yan ta'adda suka farmaki gidan yarin Kuje cikin dare
  • Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da bincike don gano wadanda suka tsere tare da kokarta dawo dasu magarkamar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Daily Trust ta ce, Hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya ta bayyana neman wasu kasurguman mutane 64 ruwa a jallo da suka tsere daga fashin magarkamar Kuje ta babban birnin tarayya Abuja.

Dangane da bayanin da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Abubakar Umar ya fitar, wadanda suka tsere an ce ‘yan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ne.

'Yan Boko Haram da suka tsere: Ana nemansu ruwa a jallo
Fashin magarkamar Kuje: FG ta fitar da bayanan 'yan Boko Haram da suka tsere | Hoto: ait.live
Asali: UGC

Idan baku manta ba, an samu hargitsi yayin da wasu 'yan ta'adda suka farmaka gidan yarin tare da sakin fursunoni daruruwa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan ISWAP sun fitar da bidiyo, sun ce su suka kai farmaki magarkamar Kuje

Daga baya wani bidiyo ya yadu, inda kungiyar ISWAP ke ikrarin kai harin, tare da nuna lokacin da take aiwatar da barnar kai tsaye.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnati ta yi Allah wadai, kana ta ce ta ji kunyar yadda jami'an tsaro suka bari haka ta faru, kamar yadda muka ruwaito a baya.

A halin da ake ciki, Hukumar ta ce ya zuwa yanzu an sake kama fursunoni 443, kuma ana ci gaba da bincike don gano sauran.

Kalli hotunansu kamar yadda AIT ta yada:

'Yan Boko Haram da suka tsere: Ana nemansu ruwa a jallo
Fashin magarkamar Kuje: FG ta fitar da bayanan 'yan Boko Haram da suka tsere | ait.live
Asali: UGC

'Yan Boko Haram da suka tsere: Ana nemansu ruwa a jallo
Fashin magarkamar Kuje: FG ta fitar da bayanan 'yan Boko Haram da suka tsere | Hoto: ait.live
Asali: UGC

'Yan Boko Haram da suka tsere: Ana nemansu ruwa a jallo
Fashin magarkamar Kuje: FG ta fitar da bayanan 'yan Boko Haram da suka tsere | Hoto: ait.live
Asali: UGC

'Yan ISWAP sun fitar da bidiyo, sun ce su suka kai farmaki magarkamar Kuje

A tun farko, kungiyar ‘yan ta’addan SWAP ta dauki alhakin harin da aka kai gidan yarin Kuje da ke Abuja, rahoton Daily Trust.

Rahotanni a baya sun bayyana yadda ‘yan ta’adda suka kutsa cikin gidan yarin, a daren ranar Talata, inda suka saki fursunoni sama da 800, ciki har da manyan mutane da ke tsare a ciki.

Kara karanta wannan

Da duminsa: An cafke 'yan gidan yari 100 da suka arce daga kurkukun Kuje

A wani faifan bidiyo da aka gani a daren Laraba, kungiyar ta'addancin ta nuna wasu daga cikin mutanenta suna harbi kan hanyarsu ta shiga cikin ginin magarkamar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel