Hotuna: Yadda aka yi bikin naɗin sarautar riƙaƙen ɗan ta'addan da FG ke nema ido rufe

Hotuna: Yadda aka yi bikin naɗin sarautar riƙaƙen ɗan ta'addan da FG ke nema ido rufe

  • Masarautar 'Yandoton Daji ta karamar hukumar Tsafe ta yi wa rikakken 'dan ta'adda da gwamnatin tarayya ke nema ido rufe, sarauta
  • Ado Aliero, fitaccen 'dan ta'adda ya samu sarautar Sarkin Fulani daga sabuwar masarautar Sarki Mai Martaba Aliyu Marafa
  • Rundunar 'yan sanda ta saka ladar N5 miliyan ga duk wanda ya kai Aliero hannun hukumar sakamakon yadda ya addabi yankin Zamfara da Katsina

Zamfara - An yi wa rikakken dan ta'adda Ado Aleru, nadin sarautar Sarkin Fulani a masarautar 'Yandoton daji dake jihar Zamfara.

'Yandoton daji tana daya daga cikin sabbin masarautu biyun da gwamnatin jihar Zamfara ta kirkiro a watan Mayun da ya gabata.

Aliero
Hotuna: Yadda aka yi bikin naɗin sarautar riƙaƙen ɗan ta'addan da FG ke nema ido rufe. Hoto daga Sahara Reporters
Asali: Facebook

An kirkiro ta ne daga masarautar Tsafe. Sabon sarkin Yandoton Daji shine Aliyu Marafa.

Hukuncin bai wa shugaban 'yan bindigan sarauta ya biyo baya ne sakamakon kokarin da yayi na tabbatar da zaman lafiya tare da jagorantar yarjejeniya tsakanin masarautar da 'yan ta'addan da suka addabi karamar hukumar Tsafe.

Kara karanta wannan

Hotuna: Bayan wata 5 da aure, fitacciyar 'yar siyasa ta haifawa mijinta santalelen 'da namiji

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Aliero
Hotuna: Yadda aka yi bikin naɗin sarautar riƙaƙen ɗan ta'addan da FG ke nema ido rufe. Hoto daga Sahara Reporters
Asali: Facebook

Aliero
Hotuna: Yadda aka yi bikin naɗin sarautar riƙaƙen ɗan ta'addan da FG ke nema ido rufe. Hoto daga Sahara Reporters
Asali: Facebook

An yi nadin sarautar a fadar masarauta Yandoton Daji kuma shugaban masarautar karamar hukumar Tsafe da kwamishinan tsaro da lamuran cikin gida, DIG Ibrahim Mamman Tsafe duk sun samu halarta.

Shugaban 'yan bindigan shi ne ya jagoranci farmakin da aka kai Kadisau, wani yankin karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina inda aka halaka kusan mutum 52.

Rundunar 'yan sandan jihar Katsina a 2019 ta bayyana cewa tana nemansa ido rufe inda ta saka N5 miliyan ga duk wanda ya kawo shi.

Miyagun farmakin 'yan bindiga sun addabi Zamfara

Yankuna masu yawa a fadin jihar sun fada halin ha'u'la'i sakamakon farmakin 'yan bindiga da suke kai samame kauyuka, su sace shanu tare da sace mutane domin karbar kudin fansa.

A 2019, gwamnatin jihar ta yi yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan bindiga. Kusan sabbin motoci kirar Hilux 15 da kudi tsagwaro aka bai wa tubabbun 'yan bindiga a 2020, Sahara Reporters ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Jam'iyyar PDP ta lallasa APC a sakamakon rumfar zaɓe ta farko da aka bayyana a Osun

Duk da wadannan yarjejeniyar, yankunan jihar suna cigaba da samun farmaki inda ake sace mutane tare da halaka su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel