Harin Kuje: ‘Allah ne kadai ya cece mu’ – Abba Kyari ya bada labarin abun da yafaru

Harin Kuje: ‘Allah ne kadai ya cece mu’ – Abba Kyari ya bada labarin abun da yafaru

  • Tsohon kwamishinan yansanda DCP Abba kyari ya bayyana abun da ya faru da da su a gidan yarin Kuje a lokacin yan bindiga suka kai hari
  • Abba kyari yace tsohon gwamnan jihar Taraba Jolly Nyame, da Farouk lawal suna cikin fursununin da suka ki tserewa
  • Kashi casa'in 90% daga cikin fursunonin 1,476, dake gidan yarin Kuje ne suka tsere inji DCP Abba Kyari

Abuja - Bayan harin da yan bidigan kungiyar ISWAP suka kaiwa gidan yarin Kuje a daren ranar Talata ya lafa.

Dakataccen tsohon Mataimakin kwamshinan yansanda DCP Abba Kyari wanda fursuna ne a gidan yari ya ba da labarin abin da ya auku a ranar harin, Rahton jaridar VANGUARD.

Yace:

’Allah ne kadai ya cece mu a yau (jiya). Sama da sa'o'i biyu da mintuna 45 'yan ta'adda sama da 300 suka mamaye gidan yarin Kuje da ke Abuja dauke da bam kirar GPMGs, Bindigogin RPGs, da sauransu.

Kara karanta wannan

Kyari, Maina, tsofaffin Gwamnoni da jerin wadanda ke tsare a gidan yarin Kuje

‘’Jimillar fursunonin gidan yarin Kuje sun kai kusan 1,476, kuma 111 ne kawai daga cikin fursunonin suka ki tserewa suka yanke shawarar ci gaba da zama a gidan yarin yayin da kashi 90 cikin 100 suka tsere.
‘’Wadanda suka yanke shawarar cewa ba za su tsere ba sun hada da tsohon gwamnan jihar Taraba Jolly Nyame, Farouk lawal, Abba Kyari da yaran sa guda hudu, wani AVM mai ritaya da kuma wasu fursunoni 107 wadanda suka gaza watanni uku su kammala zaman gidan yari kamar yadda Reuben Abati.com.Ng ta rawaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kyari
Harin Kuje: ‘Allah ne kadai ya cece mu’ – Abba Kyari ya bada kabarin abun da yafaru FOTO VANGUARD
Asali: Facebook

A daren ranar Talata ne wasu ‘yan bindiga suka kai wa gidan yarin Kuje ta Abuja hari da bama-bamai, kamar yadda hukumar NCoS ta sanar wanda kungiyar yan ta'addan ISWAP suka dauki nauyin kai harin.

A wani faifan bidiyo da aka gani a daren Laraba, kungiyar ta'addancin ta ISWAP nuna wasu daga cikin mutanenta suna harbi kan hanyarsu ta shiga cikin ginin gidan yarin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan ISWAP sun fitar da bidiyo, sun ce su suka kai farmaki magarkamar Kuje

An kwashe sojojin da ke kewayen Kuje sa'o'i 24 gabanin harin gidan yarin Kuje

A wani labarin, majiyoyin tsaro, a ranar Laraba, sun bayyana cewa sojojin da aka tura yankin Kuje da kewayen magarkama, wadanda suka yiwa yankin farin sani, an sauya musu mazauni sa’o’i 24 kafin ‘yan ta’adda su kai hari gidan yarin Kuje.

Majiyar ta yi mamakin dalilin da ya sa aka kwashe su jami'an da suka san yankin sa'o'i 24 kafin harin, kuma har yanzu ba a samun wasu da suka maye gurbinsu ba har 'yan ta'addar suka far wa yankin, inji Vanguard. Sai dai kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, wa'adin da ya kamata sojojin su zauna a wannan yankin ya wuce kuma dama ya kamata a sauya su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel