2027: Shugaban Majalisa Ya Bayyana Abin da Ya Zama Dole ga 'Yan Najeriya kan Tinubu
- Haruna Dangyatin ya bayyana cewa dole ne mazauna Jigawa su zaɓi Bola Tinubu a zaɓen 2027, yana mai danganta goyon bayansa da addini
- Kakakin majalisar ya ce Tinubu ya taimaka wajen samar da nasarar Muhammadu Buhari a baya, don haka ya kamata Arewa ta rama wannan goyon baya
- Dangyatin ya ce ƙungiyar City Boy Movement za ta gudanar da gangamin wayar da kan jama'a ta hanyar ziyartar gidaje da al'ummomi domin tallata ayyukan Tinubu da Gwamna Umar Namadi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Jigawa - Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, Haruna Dangyatin, ya yi magana kan tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Kakakin majalisar ya bayyana cewa wajibi ne mazauna jihar su zaɓi Shugaba Bola Ahmed Tinubu a babban zaɓen shekarar 2027.

Source: Twitter
Dangyatin ya bayyana hakan ne ranar Asabar, 7 ga watan Nuwamban 2026 yayin bikin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna na jam'iyyar APC a Dutse, babban birnin jihar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Ya bayyana goyon bayan Tinubu a matsayin nauyin addini, yana mai cewa shugaban ƙasar Musulmi ne, mataimakinsa ma Musulmi ne, sannan ya nuna goyon baya ga Arewa.
Meyasa ya kamata Arewa ta goyi bayan Tinubu?
Kakakin majalisar ya tuna da rawar da Tinubu ya taka wajen taimakawa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya samu nasarar zama shugaban ƙasa.
Ya ce saboda wannan gudummawar, ya kamata al'ummar Arewa su rama irin goyon bayan da Tinubu ya ba yankin a lokacin da Buhari ke neman shugabancin ƙasa.
A kalamansa:
"Tinubu ɗan'uwanmu Musulmi ne kuma shugaba ne da ke da muradin alheri ga Jihar Jigawa.”
Dangyatin ya kuma bayyana cewa duk da cewa ba a saka Jigawa cikin jerin jihohin da Tinubu zai ziyarta a farkon shirin yaƙin neman zaɓensa ba, yanzu shugaban ƙasar zai kai ziyara jihar.
Ya ce wannan dalili ne ya sa ya kamata mazauna jihar su zaɓi Tinubu tare da goyon bayan APC a dukkan matakan zaɓe.
APC ta nuna ƙarfin shirinta a Jigawa
Dangane da shirye-shiryen jam'iyyar APC, Dangyatin ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam'iyyar na da ƙarfin da za ta iya samun nasara a zaɓe mai zuwa.
Ya danganta wannan ƙwarin gwiwa da halartar taron da tsofaffin gwamnoni, sanatoci da 'yan majalisun tarayya suka yi.
A cewarsa, yawan mutanen da suka halarci taron ya nuna irin goyon bayan da APC ke da shi a sassa daban-daban na Jihar Jigawa.
City Boy Movement za ta shiga cikin al'umma
Dangyatin, wanda kuma shi ne mai kula da ƙungiyar City Boy Movement a Jigawa, ya ce ƙungiyar za ta ƙara himma wajen wayar da kan jama'a tun daga matakin ƙauyuka da unguwanni.
Ya bayyana cewa mambobin ƙungiyar za su riƙa ziyartar al'ummomi da gidajen jama'a domin yi musu bayani kan ayyukan gwamnatin Tinubu da na Gwamna Umar Namadi.

Source: Facebook
Babbar barazanar da Tinubu ke fuskanta
A wani labarin kuma, kun ji cewa fitaccen lauya kuma mai fafutukar kare haƙƙin bil'adama, Deji Adeyanju, ya bayyana babbar barazanar da Shugaba Bola Tinubu yake fuskanta a yunkurinsa na yin tazarce.
Adeyanju ya bayyana tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin babban ƙalubalen da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke fuskanta wajen neman wa'adin mulki na biyu a zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng

