"Najeriya Za Ta Kama da Wuta," Timi Frank Ya Fito da Kuskuren INEC gabanin 2027
- Tsohon mataimakin kakakin APC, Timi Frank, ya zargi INEC da haɗa baki da gwamnati domin raunana jam'iyyar hamayya ta ADC
- Frank ya bayyana cewa katsalandan ɗin da ake yi wa jam'iyyun hamayya na iya jefa tsarin dimuƙaraɗiyyar Najeriya cikin babban haɗari
- Ya yi kira na gaggawa ga Shugaba Donald Trump, da ya saka wa jami'an hukumar INEC da alkalai takunkumin hana shiga Amurka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Lagos – Shahararren mai fafutukar siyasa kuma tsohon jigo a jam'iyyar APC, Kwamared Timi Frank, ya fitar da wata zazzafar sanarwa game da yanayin siyasar Najeriya a yanzu.
Kwamared Timi Frank ya gargaɗi hukumar INEC da gwamnatin APC kan matakan da suke ɗauka waɗanda ya ce za su iya rura wutar rikicin da za ta babbake Najeriya.

Source: Twitter
Timi Frank ya soki INEC kan ADC
Tsohon kakakin na APC ya yi wannan martani ne biyo bayan rikicin da ya kunno kai a ADC, inda ya zargi INEC da nuna son kai ga ɓangaren da zai raunana jam'iyyar gabanin zaɓen 2027, in ji rahoton Leadership.
A cikin sanarwar da ya fitar a yau Alhamis, 2 ga Afrilu, 2026, Frank ya nuna damuwa kan yadda INEC ta yanke shawarar daina amfani da shugabancin David Mark ko na Nafiu Bala Gombe a matsayin shugabannin jam'iyyar ADC na riƙon ƙarya.
Ya yi iƙirarin cewa wannan mataki ne da aka dauka da gangan domin hana jam'iyyun hamayya samun natsuwa gabanin babban zaben 2027.
A cewarsa, wannan salon katsalandan ɗin da ya fara daga jam'iyyun PDP, LP, da NNPP, yanzu ya bazu zuwa ga ADC wadda ke ƙara samun tagomashi a idon ƴan ƙasa.
Frank ya alakanta Tinubu da Abacha
Comrade Timi Frank bai yi ƙasa a gwiwa ba wajen kwatanta salon mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da na tsohon shugaban ƙasa na soja, Janar Sani Abacha, in ji rahoton jaridar Independent.
Ya bayyana cewa yadda ake amfani da ƙarfin hukuma wajen murƙushe ƴancin siyasa babban koma-baya ne ga dimuƙaraɗiyyar da aka dade ana fafutukar kafawa.
Frank ya zargi shugaban da nuna "kwadayin mulki ta kowane hali" wanda hakan ke barazana ga zaman lafiyar ƙasa, inda ya yi gargaɗin cewa irin waɗannan matakan na iya "sanyawa wuta ta babbake Najeriya" idan ba a gyara ba.

Source: Facebook
Kira ga Trump da kasashen duniya
Yayin da ya ce sashen shari'ar Najeriya yanzu ya zama makamin yaƙi ga gwamnati, Timi Frank ya yi kira ga Gwamnatin Amurka, musamman Shugaba Donald Trump, da ya tsoma baki a harkokin kasar nan.
Ya buƙaci ƙasashen duniya su sanya wa manyan jami'an INEC da wasu alƙalai takunkumin biza domin hukunta su kan abin da ya kira cin dunduniyar dimuƙaraɗiyya.
Ya jaddada cewa zaɓen 2027 yana da matuƙar mahimmanci ga ƴan Najeriya, don haka dole ne a tabbatar da cewa an bar jam'iyyun hamayya sun gudanar da ayyukansu ba tare da tsangwama ba.

Kara karanta wannan
Bayan shigar Kwankwaso cikin jam'iyyar, ADC ta fallasa makarkashiyar da ake kulla mata
Matsalar da ADC ke fuskanta yanzu
A wani labari, mun ruwaito cewa, Cif Femi Fani-Kayode ya bayyana halin ni 'ya su da jam'iyyar hamayya ta ADC za ta shiga gabanin babban zabe mai zuwa.
Kalamansa na zuwa ne bayan hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta soke sunan David Mark daga matsayin Shugaban ADC.
Femi Fani-Kayode ya bayyana cewa tabbas, ADC na iya fuskantar matsala wajen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa da INEC za ta aminta da shi.
Asali: Legit.ng

