'Malamin Musulunci' Ya Kunyata Peter Obi, Ya Yi Karin Haske da aka Ce DSS Sun Cafke Shi

'Malamin Musulunci' Ya Kunyata Peter Obi, Ya Yi Karin Haske da aka Ce DSS Sun Cafke Shi

  • Malamin addinin Musulunci daga Kaduna, Sheikh Ahmad Tijjani Umar, ya yi magana kan ikirarin cewa jami'an tsaro.
  • Sheikh Ahmad ya musanta ikirarin kama shi da DSS bayan ziyarar Peter Obi, yana karyaya labarin da cewa an yi don yaudarar mutane
  • Obi ya ce an kama malamin bayan ya karɓe shi a Kaduna, yana gargadin koma baya ga dimokuradiyya da barazana ga ’yancin faɗar albarkacin baki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Sheikh Ahmad Tijjani Umar, malamin Musulunci da ke Kaduna, ya karyata rahotannin da ke cewa DSS ta kama shi.

Hakan ya biyo bayan ziyarar Peter Obi a jihar wanda tsohon gwamnan ya ce an cafke malamin bayan ganawarsu.

Malamin Musulunci ya musanta labarin cafke shi a Kaduna
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi da Sheikh Ahmad Umar. Hoto: @PeterObi.
Source: Twitter

Peter Obi ya yi ikirarin cafke 'malami' a Kaduna

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata 24 ga watan Maris din shekarar 2026, Obi ya yi zargin cewa an kama Umar jim kadan bayan ya karɓe shi a Kaduna.

Kara karanta wannan

"Muna cikin babbar matsala," Baba Ahmed ya cire tsoro, ya yi wa Tinubu kaca kaca

'Dan jam’iyyar na ADC ya bayyana lamarin a matsayin alamar tabarbarewar dimokuradiyya, yana gargadin karuwar barazana ga ’yancin magana da bayyana ra’ayi a siyasa.

Ya ce:

“An sanar da ni cewa an kama babban malamin addini Sheikh Ahmad Tijjani Umar bayan mun gana."

Malamin ya musanta rahoton cafke shi

Sai dai a wani bidiyo da ya bazu wanda TheCable ta samu, Sheikh Umar ya musanta zargin, yana cewa ba a tsare shi ba kuma ba a cutar da shi ba.

Malamin ya bayyana cewa an gayyace shi ne kawai domin amsa tambayoyi, ya ba da hadin kai, sannan aka sake shi ba tare da wata matsala ba.

Ya ce:

“Zan yi magana domin gyara rahoton ƙarya da ke yawo, ba a tsare ni ba, an gayyace ni ne kawai, na kuma samu ’yanci”
An ƙaryata rahoton cafke malami a Kaduna
Taswirar jihar Kaduna da Peter Obi ya kai wa malamin Musulunci ziyara. Hoto: Legit.
Source: Original

Ahmad Tijjani ya shawarci magoya bayansa

Ahmad Tijjani Umar ya bukaci magoya bayansa da mazauna Kaduna su zauna lafiya, su bi doka, tare da guje wa tada hankali ko rikici saboda wannan lamari.

Ya kara da cewa:

“Kada kowa ya dauki doka a hannunsa ko ya haddasa rikici saboda nuna biyayya ga wani”.

Kara karanta wannan

Matakin farko da alkali ya dauka a zaman shari'ar El Rufai da gwamnatin Najeriya

Malamin ya kuma bukaci ’yan kasa su bi hanyoyin dimokuradiyya wajen nuna rashin jin dadi, tare da jaddada muhimmancin yin rajista da kada kuri’a.

Ya ce mafita ita ce mutane su zabi shugabanni nagari ta hanyar zabe idan lokaci ya yi, domin inganta shugabanci a kasar.

Obi ya fadi musabbabin talauci a Najeriya

Kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, ya yi tsokaci kan matsalar muguwar talauci da ake fama da ita a Najeriya.

Peter Obi ya bayyana cewa 'yan Najeriya ne da kansu suka zabi jefa kasar cikin talauci saboda irin abubuwan da suke aikatawa wanda ya jawo matsaloli da dama a kasar.

'Dan siyasar mai farin jini wajen matasa ya bayyana shawarar da aka ba shi domin ganin an gyara Najeriya yadda ya kamata da kuma sauya gwamnatin APC da ya kira ta da azzaluma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.