An Yi Amfani da Ramadan, Malaman Musulunci Sun Yi Addu'a domin Tazarcen Tinubu

An Yi Amfani da Ramadan, Malaman Musulunci Sun Yi Addu'a domin Tazarcen Tinubu

  • Wata kungiyar ‘yan kasuwa, 'Iyaloja General Movement', ta shirya addu’a na musamman domin Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027
  • Taron da aka yi a Lagos ya samu halartar sarakuna, malamai, shugabannin kasuwa da magoya bayan jam'iyyar APC
  • Kungiyar ta kuma raba tallafin abinci ga mabukata domin rage radadin da ake ciki a lokacin azumin watan Ramadan mai alfarma

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos - Wata kungiya mai suna 'Iyaloja General Movement' ta shirya zaman addu’a domin shugaba Bola Tinubu da gwamnatinsa a Najeriya.

Kungiyar ta shirya addu'o'in ne domin neman nasarar sake zaben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, a babban zaben shekarar 2027.

An yi wa Tinubu addu'ar neman samun nasara a zabe
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya yana jawabi ga yan Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

An yi addu'o'i ga Bola Tinubu a Lagos

An gudanar da taron ne a Lagos, inda ya samu halartar sarakuna, malamai na addinin Musulunci, shugabannin kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki a siyasa, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Daga 1999 zuwa 2026: Jerin wakilai 18 da suka fi kowa dadewa a majalisar tarayya

Haka kuma, magoya bayan jam’iyyar APC da shugabannin al’umma daga sassa daban-daban sun halarci taron domin nuna goyon bayansu.

Taron ya kasance wani bangare na laccar Ramadan ta shekara ta tara da kuma addu’o’i na musamman da kungiyar ke shiryawa duk shekara.

Har ila yau, an gudanar da rabon tallafin abinci domin taimaka wa mabukata a lokacin azumin Ramadan.

Tinubu ya sha ruwan addu'o'i daga malamai
Shugaba Bola Tinubu yana addu'a a masallaci. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Sarakuna da suka halarci taron a Lagos

Daga cikin sarakunan da suka halarci taron akwai Oba Kamila Isiba, Olu na Agege sai Oba Ambaliu Adegbeyi, Alaige na Orile Agege da Oba Latif Egbeyemi, Ologba na Ogba.

Mai kula da kungiyar, Mutiullahi Oladeebo, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar, cewar New Telegraph.

Ya ce taron na daga cikin kokarin kungiyar na goyon bayan sake zaben Tinubu saboda irin jagorancin da yake yi.

Oladeebo ya ce kungiyar na ganin cewa matakan da shugaban kasa ke dauka za su taimaka wajen bunkasa ci gaban kasa.

Musabbabin taron addu'ar da aka yi

A cewarsa, taron ya kuma zama gangamin farkon da kungiyar za ta yi domin goyon baya ga shugaban kasa da sauran ‘yan takarar jam’iyyar a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Hadimin Osinbajo ya raba wa ADC gardama, ya fadi mutum 2 da suka dace da yin takara a 2027

Ya ce sun taru ne a cikin watan Ramadan domin neman taimakon Allah ga shugabannin kasar.

Ya kara da cewa a matsayin Musulmai suna da yakinin cewa Allah yana karbar addu’a musamman a cikin watan Ramadan mai alfarma.

A karshe, ya bayyana kwarin gwiwa cewa APC da ‘yan takararta za su samu nasara a zabe mai zuwa duba da ayyukan alheri da suke yi a kasa.

Dan ADC ya yi magana da Legit Hausa

Muhammad Salisu ya nuna damuwarsa kan yadda al'umma suka dawo kan zabe.

Ya ce abin takaici ne saboda dan abin da mutum zai samu ya manta da halin da ake ciki a kasa.

A cewarsa:

"Muna fama da tsadar rayuwa da rashin tsaro amma wasu suna neman sayar da rayuwarsu."

Ya shawarci yan Najeriya da su yi taka tsantsan saboda wannan ita ce dama ta karshe.

Limami ya yi wa Tinubu addu'a a masallaci

An ji cewa babban limami a masallacin kasa, Farfesa Luqman Zakariyah ya yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu addu'o'i bayan sallar Juma'a.

Kara karanta wannan

Amurka ta saki sunayen shugabannin Iran da take farauta, ta sanya ladar $10m

Limamin ya yi wa shugaban kasa addu'ar samun nasara a mulkinsa yayin daura auren 'ya'yan karamin ministan tsaro, Bello Matawalle.

Ya kuma roki Allah Madaukakin Sarki da ya sanya albarka a cikin wadannan aurarraki da aka daura, ya ba ma’auratan zaman lafiya a rayuwarsu ta aure.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.