Jam’iyyar PDP Ta Rasa Jigo, Gwamna Fintiri Ya Koma APC bayan zuwan Tinubu Yola
- Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya tabbatar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya
- Kakakin Majalisar Adamawa da wasu ‘yan majalisa 14 sun riga sun ajiye mukamansu a PDP wanda ke nuna jam'iyyar ta nakasa
- APC ta ce a shirye take ta karbi masu sauya sheka idan suka nemi shiga jam’iyyar ba tare da nuna masu wani bambanci ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Yola, Adamawa - Gwamnan jihar Adamawa, Umaru Fintiri, ya tabbatar da watsar da jam'iyyar PDP mai adawa a Najerya domin marawa Bola Tinubu baya a 2027.
Fintiri ya tabbatar da da ficewarsa daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya kwanaki bayan ziyarar Bola Tinubu zuwa Adamawa.

Source: Facebook
Fintiri ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gabatar wa al’ummar Adamawa ta gidan rediyo a ranar Juma’a 27 ga watan Fabrairun 2026, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan
Atiku da jagororin adawa a Najeriya sun cimma matsaya kan sabuwar dokar zabe ta 2026
Kakakin majalisa ya share fagen shiga APC
Wannan sauyin sheka na zuwa ne bayan Kakakin Majalisar Adamawa, Wesley Bathiya, ya sanar a zaman majalisa cewa shi da wasu ‘yan majalisa 14 sun fice daga PDP.
Kakakin ya karanta wasikun murabus dinsu daya bayan daya bayan kammala harkokin majalisa, inda ya tabbatar da ficewarsu daga jam’iyyar mai mulki.
Daya daga cikin ‘yan majalisar da suka sauya sheka, Mahmud Kallamu, wanda shi ne shugaban kwamitin yada labarai na majalisar, ya bayyana matakin a matsayin dabarar siyasa.
Wani dan APC ya ce jam’iyyar za ta karbi duk masu sauya sheka idan suka yanke shawarar komawa cikinta, cewar TheCable.

Source: Original
Gwamna ya fadi dalilin komawa APC
Gwamnan ya ce ya tafi tare da dukkan mambobin majalisar zartarwarsa, wadanda ya nada, da kuma zababbun shugabannin kananan hukumomi.
Ya ce ya dauki wannan mataki ne domin muradun al’ummar Adamawa da hadin kan kasa, yana mai jaddada bukatar kara daidaitawa da gwamnatin tarayya domin ciyar da manufofin ci gaba gaba.

Kara karanta wannan
Ana rade radin sauya shekar gwamna, shugaban Majalisa da mambobi 14 sun yi murabus daga PDP
Komawar Fintiri APC ya dawo da yawan gwamnonin jam'iyyar a Najeriya zuwa guda uku kacal yayin da ake shirin zaben 2027.
Yadda PDP ke karewa a Arewa maso Gabas
Har ila yau, a yankin Arewa maso Gabas da Adamawa take, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ne kadai ya rage a PDP.
Gwamna Agbu Kefas na Taraba shi ya fara sauya sheka zuwa APC kafin komawar Gwamna Fintiri na jihar Adamawa.
Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Gombe, Babagana Zulum da Borno da Mai Mala Buni su ne wadanda aka zaba a jam'iyyar APC.
Gwamna Kefas ya koma APC a hukumance
A baya, an ji cewa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta samu karuwa bayan shigowar gwamnan jihar Taraba zuwa cikinta a hukumance.
Gwamna Agbu Kefas ya samu tarba daga wajen Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da sauran jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Shettima ya yi jawabai a wajen karbar Gwamna Kefas zuwa APC, ya ce ya ji dadin matakin da ya dauka na shiga jam'iyya mai mulki.
Asali: Legit.ng