An Fara Nuna wa Juna Yatsa kan Wanda Ya Shirya Katin Rijistar Bello Turji a Jam'iyyar APC

An Fara Nuna wa Juna Yatsa kan Wanda Ya Shirya Katin Rijistar Bello Turji a Jam'iyyar APC

  • APC ta maida martani ga jam'iyyar hadaka, ADC kan zargin cewa ana tilastawa ma'aikatan gwamnati yin rijista da jam'iyya mai mulki
  • Mai magana da yawun APC na kasa, Felix Morka ya ce suna zargin ADC ta shirya katin shaidar da ke nuna Bello Turji ya shiga jam'iyyarsu
  • Ya ce jam'iyyar ADC ta tsorata da yadda jama'a ke tururuwar shiga APC shi yasa ta bullo da yada wadannan karerayi domin bata mata suna

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam'iyyar APC ta zargi ADC da shirya katin zama cikakken dan jam'iyya da sunan kasurgumin dan bindiga, Bello Turji.

APC ta fito fili ta dora wa jam'iyyar hadaka, ADC laifi, inda ta bayyana cewa ita ce ta hada tare da kirkirar katin rijista na bogi domin alakanta jam'iyya mai mulki da dan ta'addan.

Kara karanta wannan

Hadakar Atiku da Peter Obi ta yi babban kamu, tsohon gwamna ya shiga tafiyar ADC

Jam'iyyar APC.
Tutar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Hoto: @OfficialAapCNig
Source: Twitter

Yadda aka fara zargin Turji ya shiga APC

Jaridar Tribune Nigeria ta tattaro cewa wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan APC ta musanta sahihancin wata takardar shaidar zama mamba da ake dangantawa da Bello Turji.

Takardar shaidar, wacce ta karade kafafen sada zumunta ta nuna cewa Bello Turji ya yi rijistar zama cikakken dan jam'iyyar APC a Zamfara.

An ruwaito cewa Turji, wanda ke addabar jihohin Arewa maso Yamma musamman Zamfara, an ce ya yi rajistar zama dan APC a mazaba ta 13 da ke karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.

Sai dai tuni jam'iyyar APC ta musanta lamarin, tana mai cewa katin zama mamba da ke yawo ma bogi me kuma ba ta da alaka da jagoran dabar 'yan bindiga, kamar yadda Punch ta tattaro.

APC ta zargi ADC ta hada katin bogi

Amma a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin, Sakataren Yaɗa Labaran APC na kasa, Felix Morka, ya zargi jam’iyyar ADC da ƙirƙira tare da yaɗa wannan katin zama mamba na bogi.

Kara karanta wannan

Minista ya dauko da zafi, ya fara shirin garkame ma'aikatan Abuja a gidan yari

Morka ya fadi haka ne yayin mayar da martani kan zargin da kakakin ADC, Bolaji Abdullahi, ya yi a ranar Lahadi cewa APC na tilasta ma’aikatan gwamnati su shiga shirin rajistar da jam’iyyar ke gudanarwa.

Ya bayyana wannan zargi a matsayin ƙarya tsagwaronta, yana mai cewa manufar ADC ita ce bata suna da rage darajar fasahar rajistar mambobi da APC ta bullo da ita.

Bolaji Abdullahi.
Mai magana da yawun jam'iyyar ADC, Bolaji Abdullahi Hoto: @BolajiAbdullahi
Source: Twitter

Martanin da APC ta yi wa jam'iyyar ADC

Felix Morka ya ce:

“Saboda tsoro da fargabar yadda jama’a ke tururuwa suna yin rajista a jam’iyyar APC ta intanet, ADC ta fito da zargin da ba shi da tushe cewa ana tilasta wa ma’aikatan gwamnati yin rajista da APC.”
“Wannan zargi ƙarya ne tsagwaron gaske, kuma ana ƙoƙarin amfani da shi ne don bata suna da gurbata sahihancin tsarin rajista na jam’iyyarmu.”

APC ta ce wannan wani bangare ne na shirin yaɗa bayanan ƙarya da ADC ke yi, ciki har da ƙirƙira da yaɗa takardar shaidar bogi da ke nuna cewa wani shahararren ɗan ta’adda, Bello Turji ya shiga APC.

APC ta fadi banbancinta da 'yan adawa

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC ta bayyana shirye-shiryen da take yi domin samun masara a zaben 2027, wanda ta ce ya banbanta da na jam'iyyun adawa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya sare gwiwoyin 'yan adawa, ya haska dalilan da za su sa APC lashe zabe a 2027

Shugaban APC na kasa ya ce jam’iyyun adawa a kasar nan sun fi bata lokaci ne wajen surutu a talabijin, maimakon su mayar da hankali kan wayar da kan jama’a.

Farfesa Nentawe ya ce karfin APC ya samo asali ne daga aikin wayar da kan jama’a tun daga tushe a fadin kasar nan, ba wai yawan fitowa kafafen yada labarai ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262