'Abin da Ke Jinkirta Komawar Kwankwaso ADC bayan Abba Ya Guje Shi a NNPP'

'Abin da Ke Jinkirta Komawar Kwankwaso ADC bayan Abba Ya Guje Shi a NNPP'

  • Rahotanni sun nuna Rabiu Kwankwaso na jinkirta komawa jam’iyyar ADC saboda rashin tabbacin makomar Peter Obi a zaben 2027
  • Hakan bai rasa nasaba da rahotannin da ke cewa akwai yarjejeniya kan hadakar Obi da Kwankwaso game da zaben 2027
  • Wasu shugabannin Arewa sun gargadi Kwankwaso kada ya gaggauta ficewa NNPP har sai an tabbatar da Obi zai samu tikitin shugaban kasa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Wasu rahotanni sun yi hasashen abin da ya hana Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP komawa ADC.

Majiyoyi sun nuna cewa jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Rabiu Kwankwaso ya dakatar da shirin komawarsa jam’iyyar ADC saboda shakku kan makomar tikitin Peter Obi.

An 'gano' abin da ya hana Kwankwaso shiga ADC
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi a wurin taro. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Twitter

'Sharadin' sauya shekar Kwankwaso zuwa jam'iyyar ADC

Rahoton Punch ya ce wasu majiyoyi masu tushe suka ce hakan bai rasa nasaba da rashin tabbas game da makomar Obi.

Kara karanta wannan

Bayan Abba, Kwankwaso ya shiga tattaunawa da APC kan sauya sheka? Gaskiya ta fito

Majiyoyi daga tafiyar Kwankwasiyya da ADC sun bayyana cewa Kwankwaso ba zai sauya sheka ba matukar babu tabbacin cewa Peter Obi zai lashe tikitin takarar shugaban kasa.

An ce akwai shirin kafa haɗakar Obi da Kwankwaso domin takarar 2027 karkashin jam’iyyar ADC, inda ake zargin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ne ke jagorantar tattaunawar.

Kwamitin da ADC ta kafa game da Kwankwaso

An gano cewa ADC ta kafa kwamitin mutum uku domin tattaunawa da manyan ‘yan siyasa, inda aka ce kwamitin ya gana da Kwankwaso a Abuja.

Sai dai majiyar ADC ta ce ba a cimma matsaya ba a taron saboda wasu matsaloli da ba a warware ba, amma an yi alkawarin cimma matsaya cikin mako guda ko biyu.

Wani makusanci da Kwankwaso ya ce wasu manyan shugabannin Arewa tare da Obasanjo sun shawarce shi kada ya gaggauta komawa ADC.

Kwankwaso na jinkirta shiga ADC saboda Obi
Jagoran siyasar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso. Hoto: Rabiu Kwankwaso.
Source: Facebook

2027: Ana hasashen fifita Atiku kan Peter Obi

Majiyar ta ce ana fargabar cewa ADC na iya bai wa Atiku Abubakar fifiko, inda ake ganin Peter Obi na iya shan kaye a zaben fidda gwani.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya nemi zama mataimakin Tinubu a shirin shiga APC

Hakan ya sa Kwankwaso ke ci gaba da tuntuba da shawarwari, inda aka ce ba zai yanke hukunci ba har sai an kammala dukkan tattaunawa.

Wannan lamari na ci gaba da kulle kan masoyan Kwankwaso da Obi duba da irin dimbin al'umma da ke goyon bayansu musamman idan aka yi misali da zaben 2023 da ya gabata.

Buba Galadima ya kada hantar Tinubu a 2027

A wani labarin, jigon NNPP, Buba Galadima ya ce hadakar jam’iyyun adawa za ta kifar da APC a 2027, yana cewa Bola Tinubu ba zai iya lashe zabe ba.

Dattijon ya bayyana cewa jam’iyyun adawa sun koyi darasi daga 2023, kuma za su mara wa dan takarar da ya fi farin jini a Najeriya domin kawar da Tinubu daga mulki.

Ya ce NNPP na shirye yin kawance da jam’iyyu masu akida iri daya, yana mai jaddada cewa Rabiu Kwankwaso ne dan siyasar da ke da mabiyan gaske wanda ya ke da tasiri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.