Ministan Tinubu Ya Hango Adadin Jihohin da Za Su Koma karkashin APC kafin karshen 2026

Ministan Tinubu Ya Hango Adadin Jihohin da Za Su Koma karkashin APC kafin karshen 2026

  • Ana ci gaba da samun gwamnonin jam'iyyun adawa da ke komawa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya
  • Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris, ya bayyana cewa adadin gwamnonin APC zai karu
  • Mohammed Idris ya nuna cewa ana tururuwar shigowa jam'iyyar APC ne saboda manufofin da Shugaba Bola Tinubu yake aiwatarwa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a​, Mohammed Idris, ya yi magana kan tururuwar sauyar shekar da ake yi zuwa jam'iyyar APC.

Mohammed Idris ya nuna kwarin gwiwar cewa APC za ta karin jihohi zuwa 30 kafin karshen shekarar 2026, sakamakon yadda wasu gwamnoni daga jam’iyyun adawa ke nuna sha’awar komawa jam’iyyar mai mulki.

Mohammed Idris ya fadi jihohin da za su koma karkashin APC
Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris. Hoto: @FMINONigeria
Source: Twitter

Mohammed Idris ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin da yake jawabi a matsayin bako na musamman a wajen wani taro a birnin Maiduguri, jihar Borno.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Fayose ya fadi gwamnonin da za su rage a jam'iyyar Jam'iyyar PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa gwamnoni ke shiga APC?

A cewarsa, yawaitar sauya sheka zuwa APC na faruwa ne saboda kyawawan manufofi da shirye-shiryen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a karkashin “Renewed Hope Agenda”.

Ya ce hakan ya haifar da ingantaccen mulki, gyaran tattalin arziki, da daidaituwar darajar Naira, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.

“A halin yanzu jam’iyyarmu mai girma ta APC tana mulkin jihohi 24. Amma da yawan gwamnoni daga jam’iyyun adawa na nuna sha’awar shiga cikinta."
"Ina tabbatar muku cewa kafin shekarar 2026, za mu mallaki jihohi 30 yayin da muke shirin sake zaben Shugaba Tinubu a 2027."

- Mohammed Idris

Minista ya yabawa Shugaba Tinubu

Ministan ya yabawa Shugaba Tinubu, sojoji, hukumomin tsaro, da Gwamna Babagana Umara Zulum bisa jajircewarsu wajen yaki da ta’addanci da dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.

Mohammed Idris ya yi magana kan masu komawa APC
Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a. Hoto: @FMINONigeria
Source: UGC

Yayin da yake magana kan ci gaban jihar Borno, Mohammed Idris ya bayyana ta a matsayin “jihar da tafi juriya a Najeriya,” la’akari da kalubalen ta’addanci, hijirar jama’a, da bala’o’in da ta fuskanta cikin shekaru 10 da suka wuce.

Kara karanta wannan

Wike ya yi shagube ga masu sauya sheka daga PDP zuwa APC duk da yana tare da Tinubu

"Jihar Borno ita ce mafi juriya a Najeriya, la’akari da tsananin kalubalen da ta fuskanta cikin shekaru 10 da suka gabata. Mutanen Borno sun cancanci yabo bisa jajircewa da juriyarsu wajen shawo kan matsaloli."

- Mohammed Idris

Karanta wasu labaran kan jam'iyyar APC

Gwamnan Bayelsa ya yi murabus daga PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Bayelsa, Duoye Diri, ya raba gari da jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya.

Gwamna Diri ya bayyana cewa ya yi murabus daga jam'iyyar PDP wadda ya lashe zaben gwamna har sau biyu a karkashinta, saboda wasu dalilai.

Hakazalika kakakin majalisar jihar Bayelsa, Abraham Ngobere da ‘yan majalisa 18 na PDP sun yi murabus tare da Gwamna Douye Diri daga jam’iyyar adawa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng