Da Gaske Ganduje Zai Bar APC Ya Koma ADC? Hadiminsa Ya Tsage Gaskiya
- Kakakin tsohon shugaban jam’iyyar APC, Edwin Olofu, ya yi magana kan rade-radin cewa Abdullahi Ganduje zai koma ADC
- Ya ce Ganduje yana nan daram a APC, yana da aminci ga shugaba Bola Tinubu da shirin “Renewed Hope Agenda”
- Olofu ya kara da cewa ziyarar Ganduje ga Nentawe Yilwatda ta kasance ta jaje da na sirri, inda ya tabbatar masa da hadin kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Wasu sun fara yada jita-jitar cewa tsohon shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje zai bar jam'iyyar.
Hakan ya biyo bayan murabus da Ganduje ya yi wanda ya jawo zarge-zarge kan cewa tilasta shi aka yi.

Source: Twitter
An karyata cewa Ganduje zai koma ADC
Kakakinsa, Edwin Olofu, ya fito fili ya karyata jita-jitar da ake yadawa inda ya ce Ganduje na nan daram a APC, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya musanta rade-radin cewa Ganduje na shirin komawa ADC, bayan ya yi murabus daga shugabancin APC kimanin watanni biyu da suka gabata.
Bayan murabus dinsa a ranar 27 ga Yuni, 2025, an yi hasashe cewa Ganduje zai bar jam’iyyar tare da magoya bayansa, amma hakan ba gaskiya ba ne.
Ganduje ya ce matsalolin lafiya suka sanya shi yin murabus bayan shekaru kusan biyu a ofis, lamarin da ya ba da mamaki ga ‘ya’yan jam’iyya.
Tsohon gwamnan Kano ya hau shugabancin APC a ranar 3 ga Agusta, 2023, bayan taron gaggawa, inda ya zama shugaban jam’iyyar na shida cikin shekara 10.
Amma Olofu ya tabbatar cewa Ganduje yana nan daram a APC, kuma bai da niyyar barin shugaba Bola Tinubu da gwamnatinsa a wannan lokaci.
A wata hira da yan jarida, Olofu ya ce:
“Ganduje mamba ne na gaskiya a APC, mai aminci ga Shugaba da shirin 'Renewed Hope Agenda'.
“Kada ku saurari masu cewa zai bar jam’iyya, wannan labari ne na karya kawai, ba gaskiya ba ne kwata-kwata.”

Source: Twitter
Ziyarar Ganduje ga sabon shugaban APC
Da aka tambaye shi ko Ganduje ya gana da Tinubu bayan murabus dinsa, Olofu ya ce kawai tsohon shugaban jam’iyyar ne zai iya tabbatar da hakan.
Game da ziyarar Ganduje ga sabon shugaban APC, Nentawe Yilwatda, Olofu ya bayyana cewa wannan ziyara ta sirri ce kuma ta jaje, Dsily Post ta tabbatar.
Ya kara da cewa:
“Ganduje ya ce zai tallafa wa sabon shugaban jam’iyya duk lokacin da ake bukatar hakan, kuma Yilwatda ya nuna farin ciki sosai.”
Olofu ya ce Ganduje mutum ne mai kishin hadin kai, ba ya daga cikin masu nuna kiyayya ga wadanda suka gaje shi a mulki ba.
An shawarci Kwankwaso ya dukawa Kwankwaso
Kun ji cewa Kwamred Faizu Alfindiki ya yi magana kan siyasar jihar Kano da jita-jitar sauya shekar Rabiu Musa Kwankwaso zuwa APC.
Alfindiki ya shawarci Rabiu Kwankwaso kan yadda zai samu damar shiga APC cikin sauki ta hannun Abdullahi Ganduje.
Ya ce Ganduje mutum ne mai kyakkyawar zuciya wanda zai iya karɓar Kwankwaso idan ya nuna nadama.
Asali: Legit.ng

