Katsina: Bayan Bautawa APC na Shekaru, Sanata Yar'Adua Ya Bar Jam'iyyar, Ya Shiga ADC

Katsina: Bayan Bautawa APC na Shekaru, Sanata Yar'Adua Ya Bar Jam'iyyar, Ya Shiga ADC

  • Tsohon Sanata daga jihar Katsina kuma jigo a APC mai mulkin Najeriya ya yi murabus daga jam'iyyar
  • Sanata Abubakar Sadiq Yar’adua, ya fice daga jam’iyyar saboda gazawar gwamnati da rashin adalcin shugabancin jam’iyyar
  • Yar’adua ya bayyana cewa gwamnatin APC ta juya baya ga talakawa tare da aiwatar da manufofin tattalin arziki masu lalata rayuwar 'yan kasa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Katsina - Fitaccen ɗan siyasa daga Katsina kuma tsohon ɗan majalisar tarayya ya watsar da jam'iyyar APC.

Sanata Abubakar Sadiq Yar’Adua, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC inda ya zarge ta da rashin shugabanci.

Sanata ya bar jam'iyyar APC a Katsina
Sanata Yar'adua ya bar jam'iyyar APC ya shiga ADC a Katsina. Hoto: Mobile Media Crew.
Source: Facebook

Katsina: Tsohon Sanata ya caccaki tsarin APC

A wata wasiƙa mai zafi da Leadership ta samu, Yar’Adua’adua ya ce ba zai iya goyon bayan gwamnati mai “lalata tattalin arziki” da tauye walwalar jama’a ba.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Jam'iyyar ADC ta dakatar da ɗan majalisar tarayya mai ci a Kogi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Yar’Adua ya bayyana matsanancin takaici da jagorancin jam’iyyar da kuma zargin gazawar gwamnati a matsayin dalilin barinsa APC.

Ya soki abin da ya kira gurbatacciya kuma mummunar gwamnati mai fifita wasu ‘yan tsiraru a kan talakawan kasa da aka bari a wani hali.

Sadaukarwar da Sanata Yar'Adua ya yi ga APC

Yar’Adua ya tuna irin sadaukarwarsa a matsayin wanda ya kafa CPC da daga bisani APC don kifar da gwamnatin Goodluck Jonathan a 2015.

Ya ce

“Wadanda suka fafata da sauyi a baya sun fi gwamnatin da suka kifar da ita muni, sun mayar da APC jam’iyyar masu nuna wariya.
“Ina jin kunya zama cikin jam’iyyar da ta yi watsi da manufa ta kare hakkin talakawa."
Tsohon sanata a Katsina a bar APC zuwa ADC
Sanata Yar'Adua ya watsar da APC zuwa ADC. Hoto: Legit.
Source: Original

Zargin da tsohon Sanata ya yi ga APC

Ya zargi shugabannin APC da zama shiru yayin da ‘yan Najeriya ke fuskantar kashe-kashe, fyade, da korar jama’a daga gidajensu.

Kara karanta wannan

Masana'antar fina finan Najeriya ta yi rashi, matashiyar jaruma ta riga mu gidan gaskiya

A cikin wasiƙarsa, Yar’Adua ya ce yanzu masu mulki sun zama “barayin birane,” ko kuma “barayi cikin gwamnati,” kamar yadda Nasir El-Rufai ya faɗa.

Sanata ya bukaci masoyansa su dawo ADC

Yar’Adua ya ce ficewarsa daga jam’iyyar APC ta fara aiki nan take, yana kuma kiran magoya bayansa su biyo shi zuwa jam’iyyar ADC.

Ya bayyana ADC a matsayin jam’iyyar da ke da niyyar canza yanayin siyasa da dawo da martabar Najeriya da darajarta.

Ficewar Yar’Adua daga APC na nuna ƙara nuna yadda manyan ‘yan siyasa suka fusata kan yadda gwamnati ke tafiyar da tsaro da tattalin arziki.

Sanata Kingibe ta koma jam'iyyar ADC a Abuja

A baya, mun ba ku labarin cewa jam'iyyar LP mai adawa a Najeriya ta rasa ɗaya daga cikin sanatocin da take da su a majalisar dattawa.

Sanata Ireti Kingibe mai wakiltar babban birnin tarayya Abuja ta sanar da ficewarta daga LP zuwa jam'iyyar ADC da ke adawa a siyasar Najeriya.

Ireti Kingibe ta bayyana cewa za ta shirya shagali na musamman domin a yi murnar komawarta ADC inda ta soki tsarin jam'iyyar LP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.