Jam'iyyar Kwankwaso Ta Yi Babban Rashi, Ɗan Takarar Gwamna a NNPP Ya Yi Murabus
- Tsohon dan takarar gwamna na NNPP a Ondo, Hon. Olugbenga Edema, ya fice daga jam’iyyar saboda rashin gaskiya da rikice-rikicen cikin gida
- Edema ya ce cikin shekaru 35 da yake siyasa, bai taba ganin jam’iyya mai cin amanar dan takararta ba
- Ya bayyana cewa daga ranar 9 ga Mayu, 2025, ya daina zama memba na NNPP, yana mai cewa ya koyi darasi sosai
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Akure, Ondo - Jam'iyyar NNPP ta yi babban rashin jigonta wanda ya yi mata takarar gwamna a zaɓen 2024.
Dan takarar kujerar gwamna a jam’iyyar a zaben ranar 16 ga Nuwamba, 2024 a Ondo, Hon. Olugbenga Edema ya fice daga jam’iyyar.

Asali: Facebook
NNPP ta rasa babban jigo a Ondo
Edema ya aika da takardar ficewarsa ga shugaban jam’iyyar na mazabarsa ta Mahin 11, karamar hukumar Ilaje, cewar rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Edema ya ce bai taba ganin jam’iyyar da “mai cin amana" kamar NNPP ba tun da yake siyasa shekaru fiye da 30.
Dan takarar jam'iyar NNPP ya sha kaye a hannun gwamna mai ci, Hon. Lucky Aiyedatiwa, a zaben gwamna da aka gudanar a jihar.
A cikin takardar ficewa, Edema ya bayyana rashin jajircewa daga bangaren jam’iyyar a matsayin dalilin ficewarsa daga jam’iyyar.
A cewarsa:
“Tun cikin fiye da shekaru 35 da na shafe ina siyasa, ban taba ganin jam’iyya mai cin amanar dan takararta irin haka ba.
"Tsarinta ya sabawa ka’idojin jam’iyyun siyasa wadanda manufarsu ita ce kafa gwamnati a matakai daban-daban, zan so in sanar da ku cewa daga yau, na fice daga jam’iyyar.
“Tun shiga ta jam’iyyar a watan Yunin 2024, jam’iyyar ta kasance cike da rikice-rikice da rashin daidaito da ya hana ta ci gaba.

Asali: Original
Edema ya soki tsarin jam'iyyar NNPP
Edema ya yi mamaki a ce jam'iyya mai burin lashe zabe za ta kasance haka wanda ke nuna alamu na rashin tsari, cewar New Telegraph.
Ya ce:
“Bai kamata jam’iyya mai burin lashe zabe ta kasance haka ba; wannan alama ce da ke nuna rashin tsari da shirin nasara.
“Daga wadannan abubuwa, na fahimci cewa bana tare da shugabannin jam’iyyar kan yadda jam’iyya ya kamata ta kasance.
“Saboda haka, ta wannan wasikar, daga yau, 9 ga Mayu, 2025, ban sake kasancewa memba na NNPP ba."
Tsohon dan takarar bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba tukuna, amma ya ce lallai ya koyi darasi mai muhimmanci daga wannan kwarewar.
NNPP ta dakatar da ɗan takararta a Ondo
Kun ji cewa jam’iyyar NNPP a Ondo ta dakatar da tsohon dan takarar gwamna, Olugbenga Edema da mataimakinsa Rotimi Adeyemi.
Shugaban NNPP na Ondo, Peter Olagookun, da wasu jiga-jigan jam’iyyar 12 ne suka sanya hannu kan takardar dakatarwar.
An ce Edema ya kai jam’iyyar kotu ba tare da tuntubar shugabanni ba, ya kuma shiga harkokin da ke cin amanar NNPP.
Asali: Legit.ng