Dakatar da Kawu Sumaila da 'Yan Majalisa 3 Ya Bude Sabuwar Baraka a NNPP
- Tsagin jam'iyyar NNPP ya nesanta kan shi daga dakatarwar da aka yi wa Sanata Kawu Sumaila da wasu ƴan majalisar wakilai guda uku a Kano
- Sakataren yaɗa labarai na ƙasa na NNPP ya bayyana cewa dakatarwar ba komai ba ce aikin ƴan Kwankwasiyya waɗanda tuni suka raba gari da su
- Oginni Olaposi ya nuna cewa ba a sanar da kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam'iyyar ba, dangane da zarge-zargen da ake yi wa ƴan majalisun
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Jam’iyyar NNPP ta yi magana kan dakatarwar da aka yi wa Sanata Kawu Sumaila da wasu ƴan majalisar wakilai guda uku a jihar Kano.
Jam'iyyar NNPP ta bayyana dakatarwar da aka yi wa Sanata Kawu Sumaila da wasu ƴan majalisun wakilan tarayya a matsayin mara inganci.

Asali: Twitter
Sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam’iyyar NNPP, Dr. Oginni Olaposi, ya bayyana hakan yayin da yake martani kan dakatarwar a ranar Talata, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa dakatarwar ba komai ba ce face wani yunƙuri na ɓata sunan jam’iyyar NNPP ta asali.
Reshen NNPP a Kano ya dakatar Kawu Sumaila
Reshen jam’iyyar NNPP na jihar Kano dai ya sanar da dakatar da Kawu Sumaila, wanda ke wakiltar Kano ta Kudu a majalisar dattawa, tare da wasu ƴan majalisar wakilai guda uku a ranar Litinin.
Waɗanda aka dakatar ɗin sun haɗa da Hon. Ali Sani Madakin Gini, Hon. Sani Rogo, da Hon. Kabiru Alhassan Rurum.
Me NNPP ta ce kan dakatar da ƴan majalisun?
Olaposi ya ce ba a sanar da kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam’iyyar ba, kan zargi na cin amanar jam’iyyar da ake cewa ƴan majalisar sun aikata.
A cewarsa, mutanen da suka bayyana dakatarwar suna cikin ƙungiyar Kwankwasiyya, wacce yarjejeniyar hadin gwiwarta da NNPP a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ta daɗe da zuwa ƙarshe.
"Ba ma son wata ƙungiya da ba ta girmama doka ta kawo ruɗu ga ƴan Najeriya."
"NNPP tana sake jaddada cewa ƙungiyar Kwankwasiyya da ke ƙarƙashin jagorancin Sanata Rabiu Kwankwaso ba ta da ikon aiwatar da wani hukunci ko magana a madadin jam’iyyar."
"Don haka, NNPP na buƙatar jama’a, musamman mambobi da al’ummar Kano, da su yi watsi da duk wani abu da ƴan ƙungiyar waɗanda ke kiran kansu a matsayin ƴan jam'iyyar ne suke cewa."
"Sanarwar da suka fitar ba gaskiya ba ce kuma tana da nufin yaudarar jama’a. Muna nesanta jam’iyyar NNPP daga duk wata magana maras tsari da ka iya haifar da tashin hankali a jihar Kano.”
- Oginni Olaposi
A ƙarshe, Oginni Olaposi ya buƙaci hukumar tsaro ta DSS da ta gayyaci duk waɗanda ke haddasa rikici domin su amsa tambayoyi.
Ɗan majalisa ya soki dakatar da shi daga NNPP
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Rano, Bunkure da Kibiya, Kabiru Alhassan Rurum, ya yi watsi da dakatarwar da aka yi masa daga jam'iyyar NNPP.

Kara karanta wannan
Rikicin NNPP: Dan majalisa ya yi martani kan dakatarwar da aka yi masa, ya yi fallasa
Kabiru Alhassan Rurum ya bayyana cewa jam'iyyar ba ta da hurumin ɗakatar da shi domin yana wani ɓangare ne daban na NNPP ba na Kwankwasiyya ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng