'A Dawo Mulkin Buhari': Malamin Musulunci Ya Yi Addu'a ga Masu Neman Kawo Tinubu a 2027

'A Dawo Mulkin Buhari': Malamin Musulunci Ya Yi Addu'a ga Masu Neman Kawo Tinubu a 2027

  • Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Murtala Bello Asada, ya magantu kan shirye-shiryen zaben 2027, yana jan hankalin al'umma kan abin da ke tafe
  • Malamin ya koka kan yadda ake kokarin tallata Bola Tinubu a zaben 2027, yana fadin cewa Allah ya tarwatsa masu wannan shiri
  • A cikin wani bidiyo da ya wallafa a Facebook, malamin ya ce Allah ya taimaki masu nufin alheri, ya kuma magance masu son tada fitina
  • Malamin ya ce duk da yake Buhari ya rikita kasa, a yanzu lamarin ya fi muni, inda ya yi addu’ar dawowa da zaman lafiya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Sokoto - Fitaccen malamin Musulunci a jihar Sokoto, Murtala Bello Asada ya magantu kan shirye-shiryen zaben 2027 da ke tafe.

Sheikh Asada ya koka kan yadda wasu ke kokarin tallata Bola Tinubu a zaben 2027 inda ya yi musu ruwan addu'o'i.

Kara karanta wannan

Izala ta yi martani kan zargin raba Sheikh bin Usman da masallacinsa a Kano

Sheikh Bello Asada ya caccaki masu neman tallata Tinubu a 2027
Sheikh Murtala Bello Asada ya ce tattata hodar iblis ta fi sauki kan tallen Bola Tinubu a 2027. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Malam Murtala Bello Asada.
Asali: Facebook

2027: Sheikh Asada ya magantu kan zaben Tinubu

Malamin ya fadi haka a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Talata 21 ga watan Janairun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shehin malamin ya yi addu'ar Allah ya tarwatsa duk masu shirin sai sun dankara wa al'umma kansu da ƙarfi a 2027.

Ya ce idan mutum ya ce akwai gwamnati a Arewacin Najeriya sai a ce kawai ta Bello Turji ce saboda ikon da yake da shi.

Shehi ya soki salon mulkin Bola Tinubu

"Kun san akwai malamai suna nan suna shirin dauko tallen Bola Tinubu? ban san ta inda za su tallata shi ba."
"Na fada muku tallan hodar iblis ta fi sauki kan tallata Bola Tinubu a Arewacin Najeriya."
"Wai abin da suke cewa Buhari shi ya rikita kasa, ni abin da nake cewa a mayar da mu lokacin Buhari, fetur ya koma yadda yake lokacin Buhari."

Kara karanta wannan

Malami ya faɗi jihohi 8 da ƴan bindiga ke shirin kai hari, ya ce rayuwar sarki na cikin haɗari

- Sheikh Murtala Bello Asada

Sheikh Asada ya yi addu'o'i kan masu bakar aniya

Malamin ya yi ruwan addu'o'i ga masu neman tarwatsa yankin Arewa da ma Najeriya baki daya da cewa Allah ya yi maganinsu.

"Duk mai nufin wannan kasa da alheri duk inda ya ke Allah ka taimake shi duk wanda ke nemanta da sharri Allah ka tarwatsa shi."

- Malam Bello Asada

Malamin ya koka kan yadda Bello Turji ya samu iko har yake ba hukumomin Najeriya umarni kan sakin yan uwansa ko ya zafafa hare-hare kan al'umma.

Yan bindiga sun kai hari gidan Sheikh Asada

Mun ba ku labarin cewa babban malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Musa Ayyuba Lukuwa ya yi martani bayan harin yan bindiga gidan Sheikh Murtala Bello Asada.

Sheikh Lukuwa ya jaddada bukatar al'umma su bi duk hanyar da ta dace ta doka domin mallakar bindiga saboda yanayin tsaro musamman a yankin Arewa.

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala ya sha rubdugu yayin bayani kan bikin 'Qur'anic Festival'

Shahararren malamin ya ce idan da ba don Sheikh Asada ya mallaki bindiga ba kuma yi harbi da bindiga ba da yanzu wata maganar ake yi ba wannan ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.