'Ana Binciken Baffa Bichi bayan Dakatar da Shi a Sakataren Gwamnatin Kano,' NNPP
- Jam’iyyar NNPP ta tabbatar da cewa tsohon SSG na Kano, Abdullahi Baffa Bichi da Muhammad Diggol suna nan kan dakatarwa har yanzu
- Shugaban jam’iyyar a jihar ya bayyana cewa bincike kan tuhumar rashin da’a da amfani da ofis ba daidai ba yana nan yana gudana
- NNPP ta tabbatar da cewa ba ta da hannu kan matakin da gwamnatin jihar ta dauka kan wadanda aka dakatar din ko sauya musu ofis
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Jam’iyyar NNPP ta ce har yanzu tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano (SSG), Abdullahi Baffa Bichi da Kwamishinan Sufuri, Muhammad Diggol suna kan dakatarwa.
Jam'iyyar ta ce sauye sauyen da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi ba zai shafi binciken da ake kan tuhumarsu ba.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa shugaban jam’iyyar a jihar, Hashim Sulaiman Dungurawa ya ce bincike da ake musu yana nan yana yana ci gaba.
Matsayar NNPP kan dakatar da Baffa Bichi
Rahoton Trust Radio ya nuna cewa Hashim Sulaiman Dungurawa ya bayyana cewa jam’iyya da gwamnati ba daya ba ne, kuma kowanne yana da nasa aikin.
“Abin da ke faruwa ga wadanda aka dakatar din a cikin gwamnati ba shi da alaka da abin da jam’iyya take yi.
"Gwamnati ta yi abin da ta ga ya dace, mu kuma muna gudanar da namu bangaren.”
- Hashim Sulaiman Dungurawa
Matakin da NNPP za ta dauka a kan Bichi
Dungurawa ya jaddada cewa NNPP za ta jira kammala bincike kan wadanda aka dakatar kafin daukar matakin karshe.
Dakatar da Bichi da Diggol ya taso ne a daidai lokacin da ake rikicin cewa tsohon gwamnan jihar,Rabiu Musa Kwankwaso yana jagorantar jihar ta bayan fage.
NNPP ta zargi Ganduje da karya doka
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar adawa ta NNPP ta zargi shugaban APC na kasa da amfani da karfin mulki kan 'yan adawa.
Kakakin jam'iyyar NNPP, Johnson Ladipo ya yi zargin cewa ana son yin amfani da jami'an tsaro wajen kama wani jami'in gwamnati a Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

