Yahaya Bello: Sanata Ya Yi Maganar Yiwuwar Tsige Ganduje Daga Shugabancin APC

Yahaya Bello: Sanata Ya Yi Maganar Yiwuwar Tsige Ganduje Daga Shugabancin APC

  • Alex Kadiri ya yi Allah-wadai da masu kiran a nada Yahaya Bello ya zama sabon shugaban APC na kasa
  • ‘Dan siyasar ya ce gwamnatin Bello ta kawo cibaya a Kogi, bai tunanin ya cancanta da rike APC NW
  • Tsohon sanatan na Kogi bai goyon bayan tsohon gwamnansa ya maye gurbin Abdullahi Umar Ganduje

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Tsohon Sanatan gabashin Kogi, Alex Kadiri ya caccaki magoya bayan Yahaya Bello da ke nema masa wuri a APC NWC.

Vanguard ta rahoto Sanata Alex Kadiri yana mai bayyana rade-radin tsige Abdullahi Umar Ganduje a matsayin abin babban dariya.

Ganduje da Yahaya Bello
Abdullahi Umar Ganduje da Yahaya Bello Hoto: Abdullahi Umar Ganduje/kogistate.gov.ng
Asali: UGC

‘Dan siyasar yana ganin masu huro wuta a kori shugaban APC na kasa domin kawo Yahaya Bello, makiyan jam’iyya mai-ci ne.

Kara karanta wannan

Adadin kujerun APC a Majalisa ya bayyana da surukin tsohon Sanata ya zama Sanata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu so a cire Ganduje ko makiyan APC

Kadiri ya zargi masu kiran da yakar APC ta cikin gida kokarin ganin bayan jam’iyyar lokacin da fastocin Bello suka fara yawa a Abuja.

Dattijon wanda yana cikin iyayen APC musamman a jihar Kogi ya yi tir da rikon da Yahaya Bello ya yi na shekaru har takwas a ofis.

Ganduje: Sanata ya soki mulkin Bello

Sanata Kadiri wanda ya wakilci Kogi a majalisar dattawa tsakanin 1999 da 2003 ya ce APC ta kawo masu ci baya a mulkin Bello.

Duk abin da yake faruwa, ‘dan siyasar ya ce bai damu da gwamnatin Bola Tinubu ba, yake cewa halin jihar Kogi ne kawai gabansa.

“Alex Kadiri bai kwadayin mukami. Na yi Darekta Janar, na zama Sanata, shugaban majalisar kula da jami’a da babban sakatare,"

Kara karanta wannan

Kitimurmura: Akwai yiwuwar Kwankwaso da Abba su koma APC, zaben intanet ya nuna alama

"Mai kuma zan nema da Ubangiji bai yi mani ba?"

- Alex Kadiri

An rahoto Kadiri yana zargin Yahaya Bello da cin mutuncin Ata Igala da Sanata mai-ci kafin ya sauka saboda yana rike da mulki.

Bello ya dace da zama shugaban APC?

"Ba mu da kima ne? Yanzu fastocin tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello sun cika Abuja, yana so ya canji Ganduje."
"Ta ya za mu burma daga wannan gazawa zuwa wannan?"

- Alex Kadiri

A wani rahoton dabam, an ji cewa kwamishinan jihar Yobe wanda suruki ne ga Ministan harkokin ‘yan sanda zai zama sabon Sanata.

Mahaifin mai dakin tsohon gwamna Ibrahim Geidam watau Musa Mustapha zai canje shi a majalisa bayan nasarar da ya samu a APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel