Da Yiwuwar INEC Ta Cire Atiku daga cikin ‘Yan Takarar Shugaban Kasa a Makon Gobe
- INEC ta ce za ta yanke shawara kan rikicin shugabancin jam’iyyar ADC a mako mai zuwa bayan nazarin hukuncin kotu
- Wani kwamishinan hukumar, Mohammed Haruna, ya ce za su jira sai sun samu takardun hukuncin kafin ɗaukar mataki
- Hakan na zuwa ne bayan kotu ta soke shugabancin David Mark, wanda hakan zai shafi duk wanda aka ba takara a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana cewa za ta tattauna game da rikicin shugabancin jam’iyyar ADC
A mako mai zuwa ne manyan INEC za su yi zama don a yanke shawarar matakin da za ta ɗauka kan hukuncin kotu da aka yi kwanan nan.

Source: Twitter
Hukumar INEC za ta zauna kan rigimar ADC
Daily Trust ta ce kwamishinan INEC mai kula da yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe ya yi maganar halin da ake ciki a yanzu.
Mohammed Haruna ya fito ya yi wannan bayani ne ganin kotun tarayya mai zama a Abuja ta soke shugabancin Sanata David Mark.
Don haka kwamishinan ya ce hukumar ba za ta ɗauki wani mataki ba har sai ta samu ainihin takardun hukuncin kotu da ake kira CTC.
Rikicin David Mark da Nafiu Bala a ADC
Kotun Tarayya da ke Abuja, ƙarƙashin Mai Shari’a Peter Lifu ba ta yarda da shugabannin jam’iyyar ADC ba kuma ta rusa ‘yan takaransu.
Hukuncin ya ruguza zaɓen fitar da gwani da ya samar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takara.
Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar, Nafiu Bala Gombe, ya shigar yana ƙalubalantar su David Mark.
INEC tana jiran CTC kafin yi wa ADC hukunci
Mohammed Haruna ya ce INEC na buƙatar samun takardar hukuncin kotun domin lauyoyinta su gani kafin a iya yanke wani hukunci.
PM News ta ce sai lauyoyi sun ga takardun hukuncin, sun yi nazari sannan za su ba hukumar shawarar matakin da ya dace ta ɗauka.
Haruna ya bayyana cewa yawanci ana ɗaukar kusan mako guda kafin a samu ainihin takardar hukuncin kotu bayan alkali ya gama shari’a.
Ya ƙara da cewa bayan samun takardar, sashen shari’a na INEC zai nazarci hukuncin, sannan ya miƙa rahoto ga wani kwamitin hukumar.

Kara karanta wannan
"Na ƙara gane rayuwa," Sanata ya ɗauko muhimman darussa a zaman da ya yi a gidan yari
Wannan kwamiti na musamman yana ƙarƙashin jagorancin kwamishina, wanda shi kuma zai ba hukumar shawara kafin ta iya cinma matsaya.
Haruna ya ce:
"Ba za mu iya gaggauta wa kotuna ba, amma muna yin namu ɓangaren. Muna da cikakken sashen shari’a. Da zarar irin wannan hukunci ya fito, sukan je kotu domin neman takardar hukuncin."
- Muhammadu Haruna
Atiku Abubakar zai san makomarsa a makon gobe
Tsohon ɗan jaridar ya ƙare da cewa a halin yanzu INEC ba za ta iya ɗaukar wani mataki kan rikicin gidan na ADC ba har sai ta samu takardar hukuncin.
Idan an yi zama a mako mai zuwa, babu mamaki INEC ta yi wa kotu biyayya ta cire sunan ‘yan takaran ADC, a maye gurbinsu da ‘yan tsagin Nafi'u Bala.
Zuwa yanzu magoya bayan Atiku suna ta zanga-zanga yayin da ƙarar za ta shiga kotu ta gaba.

Source: Twitter
Abokin gamin Atiku Abubakar a 2023 ya bada shi
An ji labari Ifeanyi Okowa, ya koma APC ne saboda goyon manufofin Bola Tinubu da kuma gamsuwar da ya yi da sauye-sauyen gwamnatinsa.
'Dan takaran mataimakin shugaban kasar a 2023 ya ce karin kudin da jihohi ke samu a yanzu ya taimaka wajen inganta ayyukan raya kasa.
Ifeanyi Okowa bai tsaya nan ba, ya yi kaca-kaca da babban abin da Atiku Abubakar yake kamfe da shi a ADC wato dawo da tallafin fetur.
Asali: Legit.ng


