Jerin Sunaye: Majalisar Dokoki Ta Tabbatar da Sabbin Kwamishinoni 18 da Gwamnan Arewa Ya Naɗa

Jerin Sunaye: Majalisar Dokoki Ta Tabbatar da Sabbin Kwamishinoni 18 da Gwamnan Arewa Ya Naɗa

  • Majalisar dokokin jihar Kogi ta tabbatar da naɗin sabbin kwamishinoni 18 waɗanda sabon gwamnan jihar ya aiko mata
  • A wani lamari da ba a taɓa tsammani ba, Gwamna Ododo ya sanar da naɗin kwamishinonin a jawabinsa na bikin rantsarwa
  • Shugaban majalisar, Aliyu Umar Yusuf, ya ce dukkan mutanen da gwamnan ya naɗa sun cancanci yin aiki tare da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Majalisar dokokin jihar Kogi ta tantance tare da tabbatar da mutane 18 da aka nada a matsayin kwamishinonin jihar a ranar Laraba, 30 ga watan Janairu.

Sabon gwamnan jihar, Alhaji Ahmed Usman Ododo, ne ya gabatar da sunayen wadanda ya nada a matsayin kwamishinoni ga majalisar.

Kara karanta wannan

Babban labari: An rantsar da sabon mataimakin gwamnan jihar APC, sahihan bayanai sun fito

Sabon gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo.
Majalisar Dokokin Jihar Kogi Ta Amince da Nadin Sabbin Kwamishinoni 18 Na Ododo Hoto: Alhaji Usman Ododo
Asali: Facebook

Leadership ta ce a wani mataki da ba a taba ganin irinsa ba, Gwamna Ododo ya sanar da sunayen sabbin kwamishinoninsa da wasu manyan mukarrabai a wurin bikin rantsar da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ododo ya karɓi shahadar kama aiki a matsayin gwamnan jihar Kogi na biyar a tarihi ranar Asabar da ta gabata, 27 ga watan Janairu, 2024, The Cable ta ruwaito.

A wurin wannan bikin rantsuwa ne sabon gwamnan ya sanar da naɗin wasu kwamishinoni da ya ce za a tura majalisa domin tabbatar da su a matsayin mambobin majalisar zartarwa ta jiha (SEC).

Majalisar dokoki ta amince da naɗinsu

Kakakin majalisar dokokin jihar Kogi, Honorabul Aliyu Umar Yusuf, ya bukaci kwamishinonin da aka nada su yi aiki tukuru domin ci gaban jihar.

Yayin da yake karanto rahoton kwamitin majalisar, shugaban majalisar ya bayyana cewa dukkanin kwamishinoni 18 da aka nada sun cancanci yin aiki.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Majalisar dattawa ta gayyaci gwamnan babban banki CBN kan muhimman batu 2

A cewarsa gaba ɗayansu suna da kwarewa da gogewar yin aiki a matsayin mambobin majalisar zartarwa bayan tantance su.

Jerin sunayen sabbin kwamishinonin Ododo

1. Injiniya Farouk Danlami Yusuf

2. Bariata Salami Ozigi-Deedat

3. Basiru Abubakar Gegu

4. Dakta Adams Abdulaziz

5. Injiniya Joseph Oluwasegun Stephen

6. Muizideen Yinusa Abdullahi (SAN)

7. Rabiatu Okute

8. Honorabul Kingsley Fanwo

9. Fatima Momoh

10. Injiniya Mohammed Yusuf

11. Timothy Ojoma

12. Sunday Faleke

13. Mista Abanika Taye

14. Asiwaju Idris Asiru

15. Injiniya Mohammed Adbulmutalib

16. Wemi Jones

17. Mohammed Shuaibu

18. Aridajo Monday.

Kotu ta sa a kamo CoS na gwamnan jihar Ribas

A wani rahoton kuma Kotun tarayya mai zama a Abuja ta bada umarnin damke shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar Ribas, Edison Ehie.

Mai shari'a Emeka Nwite ne ya bada umarnin kama hadimin gwamna Fubara tare da wasu mutane 5 kan kona majalisar dokokin Ribas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel