Babban labari: An Rantsar da Sabon Mataimakin Gwamnan Jihar APC, Sahihan Bayanai Sun Fito

Babban labari: An Rantsar da Sabon Mataimakin Gwamnan Jihar APC, Sahihan Bayanai Sun Fito

  • Alkalin alkalan jihar Ondo ya rantsar da sabon mataimakin gwamnan jihar, Dakta Olaide Adelami ranar Alhamis, 1 ga watan Fabrairu, 2024
  • Wannan dai ya biyo bayan naɗin da Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya yi masa kuma majalisar dokokin Ondo ta amince da shi
  • A wani ɗan kwarya-kwaryar biki da aka shirya a ɗakin taro na ƙasa da ƙasa a Akure, tsohon mataimakin magatakardan majalisa ya yi rantsuwar kama aiki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Sabon mataimakin gwamnan jihar Ondo, Dakta Olaide Adelami, ya karbi rantsuwar kama aiki bayan majalisar dokokin jihar ta tabbatar da naɗinsa.

Jaridar Punch ta tattaro cewa an rantsar da tsohon mataimakin magatakardan majalisar tarayya, Dakta Adelami a matsayin mataimakin gwamnan Ondo yau Alhamis.

Kara karanta wannan

Jerin sunaye: Majalisar dokoki ta tabbatar da sabbin kwamishinoni 18 da gwamnan Arewa ya naɗa

An rantsar da sabon mataimakin gwamnan jihar Ondo.
Adelami Ya Karbi Shahadar Kama Aiki a Matsayin Mataimakin Gwamnan Jihar Ondo Hoto: Hon. Lucky Aiyedatiwa
Asali: Twitter

Idan baku manta ba, ranar Talata da ta gabata, Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya zaɓi Adelami, a matsayin wanda zai masa mataimaki bayan hawa kan mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan haka ne gwamnan ya aike da sunansa ga majalisar dokokin jihar domin tantance shi da kuma tabbatarwa.

A wani biki da aka gudanar a cibiyar al'adu da tarurruka na ƙasa da ƙasa da ke Akure a ranar Alhamis, aka rantsar da sabon mataimakin gwamnan, Dakta Adelami.

Babban alkalin jihar, Mai shari'a Olusegun Odusola, ne ya jagoranci rantsar da mataimakin gwamnan.

Adelami ya yi jawabi na farko

Da yake jawabi bayan rantsar da shi, Adelami ya yi alƙawarin yin biyayya ga Gwamna Aiyedatiwa sakamakon amintar da ya yi masa na ba shi muƙamin mataimakinsa.

Ya yi alkawarin baje kolin gogewarsa a bangarorin gwamnati da masu zaman kansu domin kawo sauyi mai amfani a jihar Ondo, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Babbar kotu ta bada umarnin kama shugaban ma'aikatan gwamnan PDP da wasu mutum 5 kan abu 1 tak

Ya ce:

"Na zo wannan muƙamin ne don hada hannu da Gwamna Lucky Orimisan Ayedatiwa wajen yi muku hidima tare da tabbatar da cewa an samar da rayuwa mai ma'ana a gare ku ta kowace fuska."

Musulmai sun koka da gwamnatin Odo

A wani rahoton kuma Al’ummar Musulmi a jihar ondo sun koka kan yadda gwamnatin jihar ke nuna wariya karara a gare su.

Suka ce gwamnan ya yi nade-nade wadanda suka saba ka’ida tare da nuna wariya ga Musulmai da ke jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel