Babbar Magana: Majalisar Dattawa Ta Gayyaci Gwamnan Babban Banki CBN Kan Muhimman Abu 2

Babbar Magana: Majalisar Dattawa Ta Gayyaci Gwamnan Babban Banki CBN Kan Muhimman Abu 2

  • Majalisar dattawa ta aike da saƙon gayyata ga gwamnan CBN kan muhimman batutuwa da suka shafi tattalin arzikin Najeriya
  • Kwamitin kula da harkokin bankuna ne ya faɗu haka jim kaɗan bayan wani zaman gaggawa da ya yi a Abuja ranar Laraba
  • Shugaban kwamitin, Sanata Abiru ya ce kowane ɗan Najeriya ya san halin da tattalin arziki ke ciki, ga faɗuwar darajar Naira

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Majalisar dattawa ta hannun kwamitin harkokin bankuna, inshora da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi, ta gayyaci gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso.

Majalisar ta aike da saƙon gayyata ga gwamnan CBN domin ya gurfana a gabanta ranar Talata mai zuwa kan yanayin tattalin arziƙin kasa da faɗuwar darajar Naira.

Kara karanta wannan

Babbar kotu ta bada umarnin kama shugaban ma'aikatan gwamnan PDP da wasu mutum 5 kan abu 1 tak

Gwamnan CBN, Cardoso.
Majalisar Dattawa Ya Gayyaci Gwamnan Babban Banki CBN Kan Muhimman Abu 2 Hoto: Centralbank
Asali: Twitter

A cewar majalisar tana bukatar Cardoso ya bayyana a gabanta domin ya yi mata ƙarin haske kan halin da tattalin arziƙi ke ciki da kuma karyewar darajar Naira a kasuwar ƴan canji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamitin kula da harkokin bankuna na majalisar karkashin jagorancin Sanata Adetokunbo Abiru (APC, Legas ta gabs), ne ya cimma matsaya ranar Laraba.

Rahoton Leadership ya nuna kwamitin ya kira zaman gaggawa ranar Laraba bayan samun labarin cewa dala ta haura N1500, bisa haka suka yanke gayyatar gwamnan CBN.

Me sanatocin suka tattauna a zaman gaggawa?

Da yake hira da ƴan jarida bayan zaman wanda ya gudana a sirri, Sanata Abiru ya ce halin da tattalin arziki ya shiga musamma hauhawar farashi ya damu majalisa.

A rahoton Guardian, Abiru, wanda tsohon manajan darakta na bankin Polaris ne, ya ce:

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An nemi Shugaban Ƙasa Tinubu ya tsige wasu ministoci kan muhimmin abu 1

"Mun yi zama yau da yammaci domin maida hankali kan inda alƙiblar tattalin arzikin Najeriya ta dosa, kowa shaida ne kan abubuwan da ke faruwa.
"Hauhawar farashin kayayyaki da sauran batutuwan tattalin arzikin da ke faruwa sun dame mu matuƙa. Mun tattauna a tsakanin mu kan batutuwa da dama.
"Kuma mun amince cewa mataki na gaba shi ne mu gayyato gwamnan CBN ya bayyana gabanmu ranar Talata da misalin ƙarfe 3:00 domin ya mana bayani kan halin da tattalin arziki ke ciki."

APC za ta ci zaɓen shugaban ƙasa a 2027

A wani rahoton kuma Mataimakin shugaban majalisar wakilai ya yi hasashen jam'iyyar da zata lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Honorabul Benjamin Kalu ya ce ya zama wajibi masu ruwa da tsakin APC na Abia su haɗa kansu domin tunkarar babban zaɓe na gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel