Ranar Farko: Sabon Gwamna Ya Bada Mukami ga ‘Danuwan Yahaya Bello da EFCC ta Cafke

Ranar Farko: Sabon Gwamna Ya Bada Mukami ga ‘Danuwan Yahaya Bello da EFCC ta Cafke

  • Ahmed Usman Ododo ya nada Ali Bello ya zama shugaban ma’aikatan fadar gwamnatinsa a Kogi
  • ‘Danuwan tsohon gwamna watau Yahaya Bello ya samu kujera a sabwar gwamnatin da aka rantsar
  • Wanda Mai girma gwamnan ya dauko ya taba fadawa hannun EFCC a zamanin mulkin ‘danuwansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Ali Bello ya zama sabon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Kogi daga hawan Mai girma Ahmed Usman Ododo.

A ranar Asabar aka rantsar da Alhaji Ahmed Usman Ododo bayan lashe zaben gwamna da aka yi a 2022 a karkashin APC.

Ododo da Ali Bello
Ahmed Ododo da Ali Bello Hoto: @OfficialOAU, @officialEFCC
Asali: Twitter

Gwamna Ododo ya kawo Ali Bello

Daga shigansa ofis a birnin Lokoja, magajin na Yahaya Bello ya sanar sunayen mukarraban da zai yi aiki da su a jiya.

Kara karanta wannan

Sabon mataimakin gwamnan Kogi ya durkusa a gaban Yahaya Bello bayan rantsar da shi, bidiyon ya yadu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ali Bello yana cikin wadanda aka nada, ya zama shugaban ma’aikatan fadar gwamnati.

A shekarar bara ku ka ji labari hukumar EFCC za tayi shari'a a kotun tarayya da wani wanda yaro ne a wajen Yahaya Bello.

Hukumar EFCC v Ali Bello

Wannan ba kowa ba ne illa Ali Bello da aka tuhuma da laifuffuka 13 na zargin karkatar da kudi daga baitul malin Kogi.

EFCC ta zargi har da Dauda Sulaiman da wani Abdulsalami Hudu da laifin satar kudin da ake zargin an juya su a BDC.

Zaman Ali Bello a gidan yari

Da farko Obiora Egwuatu ya yi hukunci a tsare wadanda ake tuhuma a gidan gyaran hali, daga baya Alkalin ya bada belinsu.

The Cable za ta iya tunawa sai da kowanensu ya biya belin N500m da jinginar gidaje na akalla N500m a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Yanzu Nan: Kwanaki 3 da Suka Wuce Tinubu Ya Saki Kudin Manyan Ayyuka 3 Inji Minista

A iyaka saninmu, daga cikin sharadin belin sai da aka karbewa Bello da sauran mutanen fasfo domin a hana su barin kasa.

Yadda aka kare a EFCC

Wadanda EFCC take kara ba su da damar yin doguwar tafiya sai sun nemi izinin kotun saboda tuhumar da ake yi masu.

Bayan lokacin EFCC ta cigaba da kiran shaidunta Junairun nan daga nan aka daga shari’ar da nufin za a cigaba a watan Fabrairu.

Hadiman Yahaya Bello a Kogi

Kafin yanzu irinsu Edward Onoja sun rike wannan matsayi, daga baya aka ji labari ya zama mataimakin gwamnan Kogi.

Da Onoja ya canji Simon Elder Achuba, sai Pharm Abdulkareem Asuku ya gaje kujerar tsohon hadimin na gwamna Bello.

Asali: Legit.ng

Online view pixel