Sheikh Pantami Ya Aiko Ta’aziyya Yayin da Aka Rasa Daya Daga Cikin Dattawan Gombe

Sheikh Pantami Ya Aiko Ta’aziyya Yayin da Aka Rasa Daya Daga Cikin Dattawan Gombe

  • Daya daga cikin dattawan jihar Gombe kuma marubuci, Gidado Bello Akko ya rasu a Zariya a jiya Lahadi, 19 ga watan Mayu
  • Farfesa Said Yunus ne ya jagoranci masa sallah a gidansa da ke Zangon Shanu Zariya kuma tuni an binne shi a makabarta
  • Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya shiga cikin jerin fitattun mutane da suka nuna alhini kan rasuwar babban marabucin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Allah ya yiwa shahararren marubuci, Gidado Bello Akko rasuwa a jiha Lahadi, 19 ga watan Mayu (11 ga watan Zul Qadah).

Pantami
Sheikh Pantami ya jajanta wa iyalan marigayi Gidado Bello Akko. Hoto: Professor Isa Ali Ibrahim Pantami/UNESCO Digital Library
Asali: Facebook

Pantami ya yi ta'aziyyar Gidado Bello

An yi jana'izar tsohon ma'aikacin wanda ya kasance daga cikin dattawan jihar Gombe a Zariya da ke jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Abin da muka sani game da hatsarin jirgin sama da ya kashe shugaban Iran

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Isa Ali Pantami ya shiga jerengiyar al'umma da suka mika sakon ta'aziyya ga iyalan mamacin a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Rasuwar Alhaji Gidado Bello Akko

Duk da cewa dan asalin jihar Gombe ne, Gidado Bello Akko ya kasance yana rayuwa ne a Zaria sakamakon aiki da ya yi a jami'ar Ahmadu Bello.

Ma'aikacin ya rasu ne a ranar Lahadi a gidansa da ke Zangon Shanu kuma an binne shi a makabartar Abatuwa a Zango da ke garin Zariya.

Farfesa Said Yunusa ya yi sallah

Limamin masallacin jami'ar ABU Zariya da masallacin ITN kuma shugaban makarantar Raudatul Furqan, Said Yunusa ya yi masa sallah.

Farfesa Said Yunusa ya yi wa'azi mai ratsa jiki a makabartar, ya yi kira ga al'ummar musulmai su shiryawa ranar da za su mutu.

Kara karanta wannan

InnalilLahi: Fitaccen Farfesa ya riga mu gidan gaskiya a Jami'ar Maiduguri

Wadanda suka halarci sallar Giddo Bello

Biyo bayan rasuwarsa, dimbin al'umma ne suka shaida sallar jana'izarsa daga ciki da wajen birnin Zariya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa cikin mutanen da suka halarci jana'izar akwai magatakardan jami'ar ABU Zariya, Rabi'u Sumaila, Farfesoshi da mutane da dama daga Gombe da Kano.

Ayyukan da Gidado Bello ya yi

Gidado Bello ya wallafa littatafai da dama ciki akwai littafin 'Koyon Karatu' da wasu littattafai da ya rubuta da harshe Fillanci tare da Hamman Tukur, kamar yadda Voice of Fulbe suka wallafa a shafin X.

A shekarar 2017, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Gidado Bello Akko a matsayin shugaban hukumar NMEC mai kula da yaki da jahilci a Najeriya.

Har ila yau, Gidado Bello Akko ya kasance tsohon suruki ne wajen tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso kuma ya mutu ya bar yara da jikoki rututu.

Kara karanta wannan

An kame satasan da suka yi amfani da bindigar sasan yara wajen Sace mota a Enugu

Pantami ya yi magana kan tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa Farfesa Isa Pantami ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda aka yi watsi da tsarin dakile matsalar tsaro a Najeriya.

Pantami ya ce a lokacin da ya ke Minista ya kawo tsarin hada lambobin NIN da layukan mutane don irin wannan matsalar amma an yi watsi da lamarin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel