Rade-radin rikici a tsakanin Yahaya Bello da Edward Onoja ya fara yawo a Kogi

Rade-radin rikici a tsakanin Yahaya Bello da Edward Onoja ya fara yawo a Kogi

Jaridar Daily Trust ta kawo wani dogon rahoto game da yadda ake zargin alakar gwamna Yahaya Bello da kuma Mataimakinsa Edward ta na kokarin tabarbarewa duk da kusancinsu.

Edward Onoja shi ne ya rikewa Yahaya Bello kujerar shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, kuma ya na cikin manyan masu juya madafan iko, kafin gwamna ya maida shi mataimakinsa.

Bayan kusan mako guda da zarcewa a kan mulki, an fara jin kishin-kishin din cewa an daina damawa da Edward Onoja a gwamnatin Yahaya Bello kamar yadda aka saba a Kogi.

A lokacin da Onoja ya ke rike da mukamin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, kusan sai wanda ya bari ne zai iya ganin gwamna, haka zalika ya na da hannu wajen nadin mukamai.

Yanzu lamarin ya fara canzawa inda har ta kai gwamna Bello ya na watsi da sunayen wadanda Mataimakin na sa ya kawo domin a ba su mukamai, ba ma wai ya ce ga yadda za ayi ba,

Jaridar ta ce Onoja ya nemi Mai gidansa ya sake nada ‘Yar garinsa Rosemary Osikoya a matsayin Kwamishina, amma gwamnan bai bi ta kansa ba, ya zakulo Mista Gabriel Yunusa Olofu.

KU KARANTA: Bello ya sadaukar da nasararsa ga tsohuwarsa bayan ya lashe zabe

Rade-radin rikici a tsakanin Yahaya Bello da Edward Onoja ya fara yawo a Kogi
Bello da Onoja sun karyata jita-jitar samun sabani a Gwamnati
Asali: UGC

Wata alama da aka gani shi ne an tsige Magajin Onoja watau Dr. Gabriel Ottah daga COS. An maida Ottah wanda Malamin makaranta zuwa ofishin mai bada shawara a kan harkar ilmi.

Wani banbanci da aka samu a gwamnatin Bello wannan karo kuma shi ne an ba ‘Ya ‘yan APC dama su kawo sunayen wadanda za a ba mukamai. Wannan zai ragewa Onoja karfi a gwamnati.

Wasu masu hasashe su na ganin cewa rigimar da ake neman farawa tun yanzu, ba ta rasa nasaba da ta takarar kujerar gwamna da za ayi a 2023, wanda ake tunanin Edward Onoja ya na hari.

Ana rade-radin cewa mulki zai koma hannun Kogi ta Yamma ne bayan wa’adin Bello. James Faleke shi ne wanda ake hangen zai zama Magajin Bello a tafiyar jam’iyyar APC a yanzu.

Watakila kuma gazawar mataimakin gwamnan wajen kawowa APC kuri’u masu tsoka a Yankin Igala ya na cikin abin da ya sa gwamna Bello ya fara watsi da Onoja bayan an lashe zabe.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng