Hukumar EFCC Ta Kai Yaron Gwamnan APC Kotu Bisa Zargin Satar Naira Biliyan 10

Hukumar EFCC Ta Kai Yaron Gwamnan APC Kotu Bisa Zargin Satar Naira Biliyan 10

  • EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta gurfanar da wani Ali Bello
  • Wannan Bawan Allah da ake zargi da laifin satar dukiyar al’umma, ‘danuwa ne ga Gwamnan Kogi
  • Bello da sauran wadanda ake tuhuma da laifi sun musanya zargin EFCC, yanzu su na gidan kurkuku

Abuja - Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, ta gurfanar da Ali Bello a gaban Alkali, ana zarginsa da satar N10bn.

A wani jawabi da ya fito daga bakin EFCC a ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba 2022, an fahimci an kai karar ne a kotun tarayya mai zama a Abuja.

Kakakin hukumar EFCC na kasa, Wilson Uwujaren ya shaida cewa shari’arsu da Ali Bello tana gaban Mai shari’a James Omotosho da yake birnin tarayya.

Kara karanta wannan

An Maka Gwamna El-Rufai da Masarauta a Kotu, Ana Neman a Tunbuke Sarkin Zazzau

Jaridar Premium Times ta ce Ali Bello ‘danuwa ne wajen Gwamna Yahaya Bello, Mai girma Gwamnan Kogi tamkar kawu yake a wajen wanda ake karar.

Hudu da Dauda Sulaiman

Sauran wadanda ake kara a kotun James Omotosho sun hada da Dauda Sulaiman, da kuma Abdulsalami Hudu wanda yake aiki a gidan gwamnatin Kogi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zargi goma yake kan Bello, Sulaiman da Hudu, a dalilin haka aka tsare su a gidan gyaran hali zuwa lokacin da za su cika sharudan belin da kotu ta bada.

Hukumar EFCC
Dauda Sulaiman da Abdulsalami Hudu Hoto: @OfficialEFCC
Asali: Twitter

Jawabin Wilson Uwujaren ya nuna Alkali ya bada belin Messrs Bello da Sulaiman a kan N1bn.

An kai kudi wajen 'yan canji

Ana tuhumar wadannan mutane da laifin cire N10, 270,556,800 daga asusun jihar Kogi, daga nan suka bada kudin ga wani ‘dan canji a Abuja, Rabiu Tafada.

Kara karanta wannan

Zulum ya Kaddamar da Yakin Neman Zabensa na 2023 a Borno

EFCC ta na zargin Bello da Sulaiman sun bukaci Tafada ya canza masu wannan N10bn zuwa kudin kasar waje domin su samu riba ta kazamar hanya.

Da aka karanto laifuffukan da ake tuhumarsu da aikatawa, ba su yarda sun aikata ba. A dalilin haka Lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo SAN ya nemi a fara shari’a.

Abdulwahab Mohammed wani babban lauya ne mai kare wadanda ake kara. Mohammed SAN ya fadawa Kotu yana son belin wadanda ya tsayawa wa.

A karshe kotu ta bada belin kowanensu kan N1bn tare da kawo filayen da darajarsu ya kai N500m. Kafin nan za a rufe su a gidan gyaran hali da yake Kuje.

Shugabar LP ta ci kudi?

A Jihar Taraba, an ji labari shugabannin Jam’iyyar Labour Party sun yi taro inda a karshe aka fatattaki Shugabar Jam’iyya saboda zarginta da laifuffuka.

Esther Gulum ta ce zarginta da cin kudi da yi wa PDP aiki duk karya ne, ta ce cikakkiyar ‘yar Obidient ce kuma mai matukar biyayya ga jam’iyyar LP.

Kara karanta wannan

ICPC Ta Kama Wani Jami'in Rundunar Tsaro Ta NSCDC Da Zamba Cikin Aminci

Asali: Legit.ng

Online view pixel