Tsohon Ministan Buhari Ya Tsoma Baki, Ya Fallasa Shirin APC Na Kwace Mulki Daga Gwamna Mai Ci

Tsohon Ministan Buhari Ya Tsoma Baki, Ya Fallasa Shirin APC Na Kwace Mulki Daga Gwamna Mai Ci

  • Tsohon ministan kwadago a mulkin Muhammadu Buhari ya ce APC ta shirya karɓe mulkin jihar Anambra a zaben 2025
  • Dakta Chris Ngige ya bayyana cewa ya san APC ta rabu gida biyu a Anambra amma zasu ɗinke ɓarakar gabanin zaben
  • Ngige ya faɗi haka ne a wurin wani taro da aka shirya a gidansa wanda aka rabawa masu ƙaramin karfi kayan tallafi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Anambra - Tsohon ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Sanata Chris Ngige, ya bayyana shirin jam'iyyar APC na karɓe mulkin wasu jihohi a zaɓe na gaba.

Ngige ya ce All Progressives Congress (APC) ta shirya kwace mulki daga hannun jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) a jihar Anambra a shekarar 2025.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba ya samu gagarumin goyon baya yayin da Kotun Koli ke dab da yanke hukunci

Chris Ngige ya ce APC zata kwace Anambra.
Jam'iyyar APC Zata Karbe Ragamar Mulkin Jihar Anambra a 2025, Ngige Hoto: Chris Ngige
Asali: Twitter

Ngige, tsohon gwamnan jihar Anambra ya yi wannan furucin ne ranar Asabar a yayin wani taro a gidansa da ke Alor, ƙaramar hukumar Idemili ta Kudu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An shirya taron ne domin rabawa mambobin jam’iyyar APC, nakasassu, da kuma tsofaffi tallafin kayan abinci, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Zamu warware saɓanin cikin gida - Ngige

Duk da ya amince cewa jam’iyyar APC ta dare gida biyua jihar, Ngige ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam’iyyar za ta yi nasara a zaben gwamna na 2025.

Tsohon ministan ya tabbatar da cewa za a warware saɓanin da ya shiga tsakanin mambobin jam'iyyar gabanin zaben gwamnan Anambra mai zuwa.

A kalamansa ya ce:

"Hakika muna da bangarori biyu a jam’iyyar APC ta jiha, ba zan musanta hakan ba. Ni duka uba ne ga kowane tsagi kuma abin duba da koyi a APC reshen Anambra.

Kara karanta wannan

Ganduje ya sake yi wa jam'iyyar PDP lahani a arewa yayin da ake jiran hukuncin Kotun Koli

"Ina sane da cewa an samu sabbin mambobin da suka haɗe da mu tun 2021. Jam’iyyar kamar coci ce; tana maraba da sabbin masu neman ceto ko kuma goyon bayan gwamnati mai ci."

Ya jaddada cewa domin samun nasara dole a yi aiki tuƙiru, inda ya kuma yi gargadi game da yin magudin zabe, yana mai cewa irin wadannan ayyuka sun zama tsohon yayi.

Ngige ya ƙara da cewa a halin yanzu yana hutawa ne, amma a watan Mayun 2025, zai yanke shawara kan matakin da zai dauka na gaba a siyasa, The Nation ta ruwaito.

NNPCL da yan kasuwa sun cimma matsaya

A wani rahoton kuma kamfanin mai na kasa NNPC da ƴan kasuwar mai sun kawo karshen raɗe-raɗin kara farashin litar man fetur a Najeriya.

Ƴan kasuwa sun nuna cikakken goyon bayansu ga matakin NNPC na barin litar mai a kan N600 da N630 ba tare an samu ƙari ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel