Ganduje Ya Sake Yi Wa Jam'iyyar PDP Lahani a Arewa Yayin Da Ake Jiran Hukuncin Kotun Koli

Ganduje Ya Sake Yi Wa Jam'iyyar PDP Lahani a Arewa Yayin Da Ake Jiran Hukuncin Kotun Koli

  • Jam'iyyar APC ta kara haifar da babban giɓi mai wuyar cikewa a jam'iyyar PDP reshen jihar Benuwai
  • Wasu manyan jiga-jigai da shugabanni akalla 9 suka jefar da tafiyar PDP, kana suka sauya sheƙa zuwa APC mai mulki
  • Kakakin PDP na jihar, Bemgba Iortyom, ya tabbatar da lamarin a wata sanarwa, yana mai yi musu fatan alheri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Wasu manyan jagororin jam'iyyar PDP na jihar Benuwai guda biyu sun sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulki.

Sakataren watsa labaran jam'iyyar PDP na jihar, Bemgba Iortyom, ya tabbatar da ficewar jiga-jigan biyu zuwa APC a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, cewar rahoton Guardian.

Kara karanta wannan

Tsohon ministan Buhari ya tsoma baki, ya fallasa shirin APC na ƙwace mulki daga gwamna mai ci

PDP da APC.
Shugabannin PDP Biyu Sun Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar APC a Jihar Benue Hoto: Official APC, PDP
Asali: Twitter

Ya ce sauya sheƙar jiga-jigan biyu, Vincent Yandev Amaabai, tsohon shugaba a matakin ƙasa da Mbakorlumun James Chia, mataimakin shugaban PDP na shiyyar B zai haifar da babban giɓi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Iortyom ya lura cewa an sanya sunayen kusoshin biyu a cikin waɗanda APC mai mulki zata ƙarɓe su a wani bikin da ta shirya yi a ranar Alhamis, 4 ga Janairu, 2024.

Ya ƙara da cewa jam'iyyar PDP tana musu fatan alheri a dukkan al'amuran da suka sanya a gaba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A kalamansa, kakakin PDP na Benuwai ya ce:

"PDP ta fahimci cewa sauya sheƙar ’yan siyasa daga tsagin adawa zuwa jam’iyya mai mulki ya zama ruwan dare a siyasarmu, kuma ba ta ga wani sabon abu ba."

APC ta shirya gagarumin taron karɓan kusoshin PDP 9

Kara karanta wannan

Zaben 2027: APC ta yi martani yayin da Atiku ya fara tunanin takarar shugaban kasa

A nata ɓangaren, jam'iyyar APC ta hannun shugaban kwamitin karɓan masu sauya sheƙa a jihar Benuwai, Becky Orpin, ta ce ta shirya ralin karɓan jiga-jigan PDP 9.

A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannunsa, APC ta jero sunayen manyan jiga-jigan PDP guda 9 da zasu baro tsagin adawa zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

A cewar sanarwan, an shirya gangamin karɓan masu sauya sheƙar ne domin karrama sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume a Yandex, karamar hukumar Gbako.

Babban Malamin Addini Ya Yi Hasashen Matsala Ga PDP

A wani rahoton kuma Primate Babatunde Elijah Ayodele na cocin INRI Spiritual Evangelical ya yi hasashen ficewar Umo Bassey Eno daga jam’iyyar PDP.

Umo Bassey Eno shine gwamnan jihar Akwa Ibom a yanzu, jihar dake a shiyyar Kudu maso Kudu mai arziƙin man fetur.

Asali: Legit.ng

Online view pixel