Kano: Gwamna Abba Ya Samu Gagarumin Goyon Baya Yayin da Kotun Koli Ke Dab da Yanke Hukunci

Kano: Gwamna Abba Ya Samu Gagarumin Goyon Baya Yayin da Kotun Koli Ke Dab da Yanke Hukunci

  • Yayin da kotun koli ke shirye-shiryen yanke hukunci, Gwamna Abba ya samu ƙarin goyon bayan jama'a a jihar Kano
  • Dubannin mambobin NNPP galibi mata a karamar hukumar Dawakin Tofa sun gudanar da addu'ar Allah ya ba Abba nasara
  • A cewarsu, kotun koli ce gatan talakawa na karshe kuma suna da yaƙinin zata yi adalci kan wanda kanawa suka zaɓa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Dandazon magoya bayan New Nigeria People’s Party (NNPP) a Dawakin Tofa da ke cikin jihar Kano sun ƙara wa Gwamna Abba Kabir Yusuf ƙwarin guiwa.

A ranar Alhamis, 4 ga watan Janairu, 2023, tulin magoya bayan NNPP na Dawakin Tofa suka gudanar da taron addu'o'in Allah ya ba Gwamna Abba nasara a kotun ƙoli.

Kara karanta wannan

Dar-dar yayin da ake sauraron hukuncin Kotun Koli a shari’ar zaben gwamnan jihar Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano.
Magoya Bayan NNPP Sun Gudanar da Addu'o'in Allah Ya Ba Abba Nasara a Kotu Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Dawakin Tofa ita ce mahaifar tsohon gwamnan jihar Kano kuma shugaban APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Ganduje, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dandazon Kanawan waɗanda galibinsu mata ne, sun ƙara jaddada goyon bayansu ga Gwamna Kabir Yusuf, tare da yin addu’o’i ya samu nasara a kotun koli.

Dubbannin mutane ne daga kauyukan Dawakin Tofa suka tattaru a masallacin Bandirawo da na Dawanau, suka yi salloli da rokon Allah ya kawo ɗauki a shari'ar zaben Kano.

Yayin da yake jawabi ga dubannin mahalarta wurin, jagoran tawagar, Idris Dandalama ya ce:

“Mun zo nan ne domin rokon Allah Madaukakin Sarki ya tabbatar mana da hakkinmu. Kotun koli ita ce gatan talaka na ƙarshe kuma muna fatan hukuncin da zata yanke ya mana kyau."

Meyasa suka fito yin addu'o'i da rokon Allah?

Kara karanta wannan

Sojojin Sama Sun Kashe Shugaban Yan Ta'adda, Ba'a Shuwa, da Wasu Mayakansa a Borno

Bugu da kari, ya bayyana jin dadinsa bisa ganin cewa a kankanin lokacin da Gwamna Yusuf ya shafe kan madafun iko, ya nuna aniyarsa ta bunƙasa Kano zuwa mataki na gaba.

A ruwayar Channels tv, jagoran taron ya ci gaba da cewa:

"Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi nasarar warware basussukan fansho da giratuti na mazajen mu da suka yi ritaya. Ya saukaka aurar da ‘ya’yanmu mata, ya riƙa biyan mu albashi a kan lokaci.
"Ya tallafawa naƙasassun mu, ya kuma ɗauki nauyin yayanmu su tafi ƙaro karatu a ƙasashen duniya. Bisa haka muka fito addu'ar neman zaman lafiya a Kano duba da yanayin siyasa da muka tsinci kanmu."

Wasu mazauna Kano da ke goyon bayan NNPP sun shaida wa Legit Hausa cewa har azumi suke yi domin Gwamna Abba ya samu nasara a kotun koli.

Malam Aminu, mazaunin Anguwar Mile 9, ya ce:

"Mun fahimci cewa ana so a yi amfani da ƙarfin mulki ne a kwace nasarar NNPP saboda wata manufa, to amma mun san Allah ke komai shiyasa muka duƙufa addu'a."

Kara karanta wannan

Miyagu sun harbe babban limamin Masallacin Jumu'a da ɗan acaɓa a Filato

"Abin da ke bani mamaki shi wanda ake son ƙaƙaba mana da farko ya hakura har murna ya taya Abba, amma yanzun saboda kwaɗayin mulki ya dawo yana so, mu dai Allah ya bayyana gaskiya."

Kabir Abdullahi da ke Ɗorayi karama ya ce:

"Ni ba ruwa da zancen shari'ar nan, abin da na sani na zaɓi NNPP lokacin zaɓe kuma mafi akasarin ƴan Kano ita suka zaɓa, ni banga dalilin kai kara ba tunda mutane sun zabi wanda suke so."

APC ta samu karuwa daga PDP a jihar Benuwai

A wani rahoton na daban Wasu manyan jagororin jam'iyyar PDP na jihar Benuwai guda biyu sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Jam'iyyar APC ta hannun shugaban kwamitin karɓan masu sauya sheƙa a jihar Benuwai, Becky Orpin, ta ce ta shirya ralin karɓan jiga-jigan PDP 9.

Asali: Legit.ng

Online view pixel