"Ba daɗi" Ɗan Marigayi Akeredolu Ya Bayyana Gaskiyar Yadda Gwamnan APC Ya Mutu, Abun Tausayi

"Ba daɗi" Ɗan Marigayi Akeredolu Ya Bayyana Gaskiyar Yadda Gwamnan APC Ya Mutu, Abun Tausayi

  • Iyalan marigayi tsohon gwamna Oluwarotimi Akeredolu (SAN) sun nuna alhini yayin da suka tabbatar da rasuwar mai gidansu
  • A cewar iyalan, marigayi Akeredolu ya rasu ne a cikin bacci yayin da yake ƙarƙashin kulawar likitoci kan cutar da ke damunsa a Jamus
  • Legit Hausa ta tattaro cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da ɗan mamacin, Oluwarotimi Akeredolu Jnr ya fitar a madadin iyalan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Tsohon gwamnan jihar Ondo da ya gabata, Rotimi Akeredolu, ya mutu ne a cikin baccinsa.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da ɗan marigayin, Oluwarotimi Akeredolu Jnr, ya fitar da yammacin ranar Laraba, 27 ga watan Disamba, 2023.

Kara karanta wannan

Aiyedatiwa: Jerin hadiman gwamna da suka yi murabus daga muƙamansu bayan mutuwa ta gitta

Marigayi gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.
Abun ba daɗi: Ɗan Marigayi Akeredolu ya bayyana yadda mahaifinsa ya cika a Jamus Hoto: Rotimi Akeredolu Aketi
Asali: Facebook

Iyalan gwamnan sun tabbatar da mutuwarsa

Akeredolu Jnr ya bayyana yadda mahaifinsa gwamnan APC ya rasu a shafin mamacin na dandalin sada zumunta Facebook a madadin iyalan gidansu gaba ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwan ta ce:

"Ya mutu cikin kwanciyar hankali yayin da yake bacci a asibiti a ƙasar Jamus, inda yake kwance yake jinyar ciwon da ke damunsa watau cutar daji."
"Duk da muna cikin alhini da kukan rabuwa da shi amma hankali na kwanciya idan muka tuna mala'ikun haske ne zasu masa jagora zuwa barzahu, waɗanda ya rayu da su a doron duniya."
"A wannan lokaci mai ƙuna da wahala, muna gode wa dukkan waɗanda suka jajanta mana tare da tausaya mana tun da labarin mutuwar ya yaɗu."
"Cikakken bayani kan tsarin yadda za a masa jana'iza da sauran shirye-shirye za a ji su daga iyalai da kuma gwamnatin jihar Ondo nan ba da daɗewa ba."

Kara karanta wannan

"Na hakura": Kwamishinan Akeredolu ya yi murabus bayan Aiyedatiwa ya zama gwamnan Ondo

Idan baku manta ba a jiya Laraba ne Gwamna Akeredolu na jihar Ondo ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da doguwar jinya. Gwamnatin Ondo ta tabbatar da haka.

Kuma tun a jiyan aka rantsar da mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa, a matsayin cikakken gwamna kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Diyar Akeredolu Ta Fattaki Yan Jarida Daga Gidan Mahaifinta

A wani rahoton na daban Ololade, diyar marigayi Gwamna Rotimi Akeredolu, ta yi yar dirama yayin da ta fatattaki yan jarida daga gidan mahaifinta da ke Ibadan.

Yan jaridan sun isa gidan marigayi gwamnan ne saboda ziyarar ta'aziyya da Gwamna Abdulrahman Abdulrasaq da Seyi Makinde suka kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel