Kwankwaso Ya Kitsa Rikicin NNPP? Babban Jigo a Jam'iyyar Ya Bayyana Gaskiya

Kwankwaso Ya Kitsa Rikicin NNPP? Babban Jigo a Jam'iyyar Ya Bayyana Gaskiya

  • Wani jigo a jam’iyyar NNPP, Adekunle Aderibigbe, ya ce ƴan jam’iyyar na son Rabiu Kwankwaso ya warware rikicin cikin gida na jam’iyyar
  • Kwankwaso dai tsohon gwamnan jihar Kano ne kuma tsohon Sanata, wanda ke da niyyar zama shugaban Najeriya
  • Da yake magana a wata hira da Legit.ng, Aderibigbe ya bayyana cewa akwai buƙatar Kwankwaso ya kawo ƙarshen rikicin domin jam'iyyar ta tsaya da ƙafafunta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Kano, jihar Kano - Adekunle Razaq Aderibigbe, jigo a jam’iyyar NNPP a jihar Legas, ya ce yawancin jiga-jigan jam’iyyar “suna koyi da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso,”.

Aderibigbe ya ce domin haka ne ma wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ke alaƙanta matsalolin da ke addabar jam’iyyar da shi.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta bayyana matsayarta kan yarjejeniya 8 da Tinubu ya cimmawa tsakanin Wike da Fubara

An shawarci Kwankwaso kan rikicin NNPP
An shawarci Kwankwaso kan yadda zai kawo karshen rikicin NNPP Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito a baya-bayan nan, shiyyar Kudu maso Kudu ta jam’iyyar NNPP ta zargi Kwankwaso, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a 2023 da haddasa rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun mataimakin shugaban jam'iyyar na ƙasa shiyyar Kudu maso Kudu, Emmanuel Nwabrije, kwamitin gudanarwa na jam’iyyar NNPP na shiyyar Kudu maso Kudu da masu ruwa da tsaki sun sake tabbatar da korar Sanata Kwankwaso.

Abin da ƴan NNPP ke so daga Kwankwaso - Aderibigbe

Amma da yake mayar da martani game da rashin jituwar da wani ɓangare na ƴan jam’iyyar NNPP, Aderibigbe ya ce wuƙa da nama na hannun Kwankwaso.

Ya shaidawa Legit.ng cewa:

"Mafi yawan ƴaƴan jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) sun zuba ido ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, suna sa ran zai tabbatar da haɗin kan jam’iyyar, shi ya sa shugabannin shiyya na jam'iyyar ke ƙara matsa masa lamba."

Kara karanta wannan

Betta Edu: Matasa marasa aikin yi sun aike da sako mai muhimmanci ga ministar Tinubu

"Babu wani dan jam’iyyar da ya ji dadin sakamakon shari’ar da kotu ta yi na gwamnan Kano, kasancewar dukkansu suna goyon bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf."
"Mambobin jam’iyyar suna son Kwankwaso ya yi magana tare da warware rikicin cikin gida a cikin jam’iyyar domin kowa ya mayar da hankali kan al’amuran da ke tsakanin jam’iyyar da jiha da jama’a."
"Da zarar Kwankwaso ya kashe wutar rikicin cikin gida ta hanyar samar da sulhu, NNPP za ta ƙara ƙarfi kuma ta zama babbar jam'iyya a ƙasa."

Kwankwaso Ya Kai Ziyara a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyarar jaje a jihar Kaduna.

Kwankwaso ya kai ziyarar ne domin jajantawa mutanen da harin bam ɗin da sojoji suka kai bisa kuskure kan masu Maulidi a ƙauyen Tudun Biri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng