Da Gaske Na Hannun Daman Atiku Ya Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC? Gaskiya Ta Bayyana

Da Gaske Na Hannun Daman Atiku Ya Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC? Gaskiya Ta Bayyana

  • Kakakin kamfe na dan takarar shugaban kasa a 2023, Daniel Bwala ya karyata jita-jitar cewa ya koma jam'iyyar APC
  • Bwala ya ce wannan karya ce tsagwaronta inda ya ce idan ya na son koma wa da kanshi zai sanar
  • Wannan na zuwa ne bayan an yi yada cewa jigon PDP ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC daga PDP wanda ya musanta hakan

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Jigon jam'iyyar PDP kuma na hannun daman Atiku Abubakar, Daniel Bwala ya musanta sauya sheka zuwa APC.

Bwala, wanda shi ne kakakin kwamitin kamfe na dan takarar shugaban kasar ya ce har yanzu ya na nan daram a PDP, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Zamfara: Babban malami ya bayyana jam'iyyar da za ta yi nasara bayan kotu ta umurci a sake zabe

Da gaske na hannun daman Atiku ya koma APC? an fayyace gaskiya
Bwala ya yi martani kan jita-jitar koma wa APC. Hoto: Atiku Abubakar.
Asali: Facebook

Mene Bwala ke cewa kan barin PDP zuwa APC?

Bwala ya musanta hakan ne a daren yau Asabar 18 ga watan Nuwamba a shafin Twitter.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Idan ina son koma wa jam'iyya mai mulki, ni da kai na zan sanar kamar yadda na yi lokacin da na bar APC zuwa PDP."

Wane martani ya yi kan jita-jitar barin PDP zuwa APC?

Bwala ya rubuta a shafin Twitter kamar haka:

"Ina tunanin hanya mafi kyau da zan karyata hakan shi ne na fito a talabijin na Tinubu don fayyace wa.
"Idan ina son tafiya jami'yya mai mulki, ni zan sanar kamar yadda na yi lokacin da na bar APC zuwa PDP."

Wannan na zuwa ne bayan yada jita-jitar cewa Bwala ya fece daga jam'iyyar PDP mai adawa zuwa jam'iyyar APC mai mulki a kasar.

Kara karanta wannan

Da hannun Tinubu, dan takarar gwamnan Kogi ya yi amai ya lashe, ya garzaya kotu neman hakkinsa

Jigon PDP ya ce kira daya Atiku zai yi a kori Wike

A wani labarin, Jigon PDP, Daniel Bwala ya bayyana cewa kirar waya daya Atiku zai yi wa Tinubu ya kori Nyesom Wike daga mukaminsa.

Bwala ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Arise a ranar Laraba 13 ga watan Satumba na wannan shekara.

Wannan martani na Bwala na zuwa ne bayan Wike ya yi barazanar korar Atiku daga jam'iyyar PDP a kwanakin baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel