"Yan maula sun fara": Jama’a sun yi caaa kan Ali Nuhu bayan ya taya Gawuna murnar nasara a kotun

"Yan maula sun fara": Jama’a sun yi caaa kan Ali Nuhu bayan ya taya Gawuna murnar nasara a kotun

  • Babban jarumin masana'antar fim, Ali Nuhu ya yi martani kan nasarar da Nasir Gawuna ya yi a kotun daukaka kara
  • Sarkin Kannywood ya taya Gawuna da mataimakinsa, Murtala Garo murnar nasara da suka yi kan Gwamna Abba Kabir Yusuf
  • Sai dai, yan soshiyal midiya sun yi wa jarumin wankin babban bargo kan aika sakon taya murna ga yan takarar na APC a zaben gwamnan jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood, Ali Nuhu, wanda aka fi sani da sarki ya yi martani bayan kotun daukaka kara ta tabbatar da Nasir Yusuf Gawuna a matsayin zababben gwamnan Kano na 2023.

A ranar Juma’a, 17 ga watan Nuwamba ne, kotun daukaka kara mai zama a Abuja ta tsige gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da soke nasarar zabensa na ranar 18 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Bayan tsige gwamnan Kano, Malamin addini ya yi hasashen sakamakon hukuncin zaben Kaduna da Nasarawa

Yan soshiyal midiya sun caccaki Ali Nuhu kan taya Gawuna murna
"Yan maula sun fara": Jama’a sun yi caaa kan Ali Nuhu bayan ya taya Gawuna murnar nasara a kotun Hoto: Dr Nasir Yusuf Gawuna/Ali Nuhu Mohammed
Asali: Facebook

Kamar yadda aka sani, masana’antar Kannywood na taka rawar gani sosai wajen tallata yan takara musamman a jihar Kano wacce take cibiyarsu. A kan samu rabuwar kai tsakanin yan fim inda kowa kan karkata zuwa wajen yan takara da yake muradi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kowa dai ya san Ali Nuhu Gawuna ya marawa baya a lokacin zaben gwamna amma suka sha kaye a wancan lokacin.

Don haka yanzu da kotun daukaka kara ta kai nasara bangaren dan takararsa, sai ya fito ya taya shi murna a shafinsa na Instagram.

Ya rubuta a shafin nasa:

“Ina taya ku murna kan nasararku a kotun daukaka kara @dr.nasirugawuna da @murtala_garo."

Jama’a sun yi wa Ali Nuhu caaa a kai

Sai dai wannan sakon taya murna da jarumin ya aikawa su Gawuna bai yi wa mabiya shafinsa da dama dadi ba inda suka fito suka yi masa caaa a kai.

Kara karanta wannan

"Siyasar ubangida": Bidiyon Ododo duke a gaban Yahaya Bello ya haddasa cece-kuce

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin mabiyansa a kasa:

official_adam_bosz:

"Toh yan maulla sun fara."

_virus__official.

"Kaima ka shiga cikin sahun kin Allah da kin qaddara."

ashalaf90:

"Abanza abanzazza ko gyezau Abba Zama daram dam da yaddar Allah."

excellenc008:

"Ban taɓa sanin jahili nake following ba sai yanzu. Oh forget! Ashe ba ɗan jihar ba ne shi ya sa zai so ƴan taɓare su karɓe ta don su tarwatsa ta. Toh Allah ya fi ku ya fi wanin ku mitsiyatan banza mitsiyatan wofi."

c.e.o_albany_enterprises:

"Wanda Yabi Bayan Zalunci Menene Hukuncinsa A Gurin Allah Director @realalinuhu."

abseed__30:

"@hafsieabdie taya zeyi yanzu munsan inda yadosa ai Daman can dan na nasune."

hafsieabdie:

"Da Abba yaci gwamna banga kayi posting dinshi ka taya sa murna ba."

syllar_lk:

"Se mun hadaka da daurawa zaka gani ai."

bn_ismail_kaware:

"Anyi walkiya fa munafukai sun fito."

maawiyya_ahmad:

"Masu Cewa supreme court GAWUNA ba zeyi NASARA ba, BAKAR ADDU'AHR ku kanku zata afka ta ruga DA tana tare da ku in SHA ALLAH a tribunal Abba ya fadi, haka appeal, to a supreme court din ma in SHA ALLAH a cikin minti 30 za'a kayar da Abba gida gida da IKON ALLAH ."

Kara karanta wannan

Hukuncin Kano da Zamfara: APC ta yi martani yayin da kotun daukaka kara ta tsige Abba Gida Gida

umar_designs:

"Wannan abun kunyane ga Jihar Kano. Wadanda aja Kama da satar kuri'a da yaga takardun zabe, yau sune aka tursasawa mutan Kano, sune zasuyi mulki. Ya Allah duk wadanda suke da hannu a cikin wannan abu, ya Allah kada kabasu ikon jin dadin zaman duniya, Allah ka sakawa talakan Kano, Amen."

mall.a9304:

"wlh wani Abu sai kazo Nigeria indai makirci da zalunci da rashin tsoron Allah sai kazo Nigeria wlh duk Dani Dan maiduguri ne Aman wlh wanan Abun baikamata ba wlh Allah dai yasa mudace Allah katar watsa azalumai a Nigeria ."

_abdoul_asi_:

"Ina ganin girmanka sarki amma Gsky ba Ka kishin knka da al umar jihar kano ko Kai daman asali ba dan kanon bne amma Ka kama girmanka."

Iliyasu Kwankwaso ya ba Abba shawarwari

A wani labarin, mun ji cewa babban jigon jam'iyyar APC, Alhaji Iliyasu Kwankwaso, ya bukaci gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya karbi hukuncin kotun daukaka kara da ta tsige shi daga kujerarsa, rahoton Nigerian Tribune.

Kotun ta tabbatar da Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin sahihin wanda ya lashe zaben gwamna na ranar 18 ga watan Nuwamba a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel