Bayan Tsige Gwamnan Kano, Malamin Addini Ya Yi Hasashen Sakamakon Hukuncin Zaben Kaduna da Nasarawa

Bayan Tsige Gwamnan Kano, Malamin Addini Ya Yi Hasashen Sakamakon Hukuncin Zaben Kaduna da Nasarawa

  • Hankula a bangaren siyasa sun karkata zuwa kotuna yayin da fusatattun yan takarar gwamna da jam'iyyun da suka yi takara a zaben 2023 suka tunkari bangaren shari'a
  • Masu kara na neman kotu ta bi masu hakkinsu don tabbatar da ganin sun cimma kudirinsu na son zama gwamna
  • Da yake magana kan wasu kararrakin zaben gwamna gabanin sauraren su a kotun daukaka kara, Primate Ayodele ya bukaci wasu yan takara da su nemi taimakon Allah

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Primate Babatunde Elijah Ayodele ya bukaci yan takarar gwamnan PDP a jihohin Kaduna da Nasarawa da su nemi taimakon Allah don nasara a kotun daukaka kara.

Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, ya aika wannan sakon ne ta shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) a ranar Juma'a, 17 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kano da Zamfara: APC ta yi martani yayin da kotun daukaka kara ta tsige Abba Gida Gida

Primate Ayodele ya magantu kan makomar zaben gwamnan Kaduna da Nasarawa
Bayan Tsige Gwamnan Kano, Malamin Addini Ya Yi Hasashen Sakamakon Hukuncin Zaben Kaduna da Nasarawa Hoto: Primate Babatunde Elijah Ayodele
Asali: Facebook

Takaddamar zabe a jihohin Kaduna da Nasarawa

Malamin addinin ya yi ikirarin cewa akwai yan rufa-ido da masu shigar da kara suka fara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta tuna cewa gwamnan Kaduna, Uba Sani, wanda ya sha da kyar a kotun zaben gwamnan jihar ya shigar da kara gaban kotun daukaka kara a watan Oktoba, kan wani sashi na hukuncin kotun zaben. Sani ya kasance dan APC.

Abokin hamayyar gwamnan a zaben na 18 ga watan Maris, Isah Ashiru na PDP, shima ya daukaka kara a bangaren da bai yi masa ba a hukuncin kotun zaben, wanda aka yanke a watan Satumba.

Hukuncin da kotun ta yanke ya tabbatar da zaben Sani, amma ta bayyana cewa da za ta iya korar gwamnan tare da ba da umarnin sake gudanar da zabe.

Kotun zaben ta bayyana cewa bata yi umurnin sake zabe bane kawai saboda Ashiru ya keta wasu ka'ida wajen shigar da kararsa.

Kara karanta wannan

'Jarabawa ce, gwamna ya yi martani kan hukuncin kotun da ta rusa zabenshi, ya sha alwashi

A Nasarawa, kotun zabe ta tsige Gwamna Abdullahi Sule a watan Oktoba, inda ta ayyana David Ombugadu na PDP a matsayin wanda ya lashe zabe.

Bayan nan, sai Gwamna Sule, jigon APC ya daukaka kara a kotun daukaka kara reshen Makurdi.

A ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba, kotun daukaka kara reshen Abuja ta tanadi hukunci kan karar da Sule ya daukaka.

Kada ku yi barci: Ayodele ga yan takarar PDP

Primate Ayodele ya bayyana a cikin bidiyon da Legit Hausa ta gano:

"Na Kaduna, suna kokarin yin wasu murdiya, suna kokarin yin wayo wayo a chan. Don haka, dan PDP (Ashiru), za ka yi nasara idan ka kara matsa lamba, kada ka yi bacci., saboda na Kadunan, suna so su ga abun da za su iya yi a kai. Kai (Ashiru) kana iya samun kuri'unka idan ka bi kai da fata. Kada ka huta."

Kara karanta wannan

Martanin yan Najeriya bayan kotun daukaka kara ta tsige Abba Gida-Gida daga matsayin gwamnan Kano

"Haka kuma Nasarawa, suna kokarin murde hukuncin. Nasarawa bata bukatar komai kuma, Kadunan bata bukatar komai, hatta Kano bata bukatar komai kuma, amma suna so su yi wasu abubuwa marasa kyau don juya shi. Don haka ku zuba ido, ku ci gaba da bi sako da sako don kada ya yi aiki."

APC ta yaba hukuncin kotun daukaka kara

A wani labarin, mun ji cewa jam’iyyar APC mai mulki ta mayar da martani kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na tsige gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano tare da ayyana zaben gwamnan jihar Zamfara a matsayin wanda bai kammala ba.

Sakataren labaran jam’iyyar APC na kasa, Felix Morka, ya yaba da hukuncin da kotun ta yanke a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng