Usman Ododo Na APC Ya Lallasa Abokan Hamayarsa a Karamar Hukumarsa Da Tazara Mai Yawa

Usman Ododo Na APC Ya Lallasa Abokan Hamayarsa a Karamar Hukumarsa Da Tazara Mai Yawa

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Okene, Jihar Kogi - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a kasa, a ranar Lahadi 12 ga watan Nuwamba, ta yi nasara a karamar hukumar Okene na jihar Kogi a zaben gwamna na 2023 a jihar.

Ododo ya lashe mazabarsa da gagarumin tazara a zaben gwamnan Kogi
Usman Ododo ya lashe karamar hukumarsa da tazara mai girma a zaben gwamnan jihar Kogi: Hoto: Usman Ododo, Dino Melaye
Asali: Facebook

A cewar Hukumar Zabe mai Zaman Kanta na Kasa (INEC), Ahmed Ododo na jam'iyyar APC ya kayar da Dino Melaye na Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da Murtala Ajaka na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) a zaben da aka yi a karamar hukumar a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Yi Garkuwa Da Jami'an INEC a Karamar Hukuma a Bayelsa

Ododo ya samu kuri'u 138,416 inda Melaye ya samu kuri'u 1,463 shi kuma Ajaka ya samu kuri'a 217.

Duba kuri'un a nan kamar yadda The Cable ta wallafa.

Masu zabe da suka yi rajista: 151,243

Masu zabe da aka tantance: 141,898

ADC: 261

APC: 138,416

PDP: 1,463

SDP: 271

Kuri'u masu kyau: 141,404

Lalatattun kuri'u: 134

Jimlar kuri'u da aka kada: 141,538

Asali: Legit.ng

Online view pixel