An Yi Garkuwa Da Jami'an INEC a Karamar Hukuma a Bayelsa

An Yi Garkuwa Da Jami'an INEC a Karamar Hukuma a Bayelsa

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Yenagoa, Jihar Bayelsa - Wani abu da za a iya kira mai hatsari ya faru da jami'an Hukumar Zabe mai Zaman Kanta na Najeriya (INEC) a jihar Bayelsa.

A halin yanzu, an tsare wasu jami'an INEC ba tare da son ransu ba a karamar hukumar Brass ta jihar Bayelsa.

Da ta ke tabbatar da lamarin, INEC cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X (tsohuwar Twitter) a ranar Lahadi, 12 ga watan Nuwamba, ta yi kira ga jami'an tsaro su yi gaggawan ganin an sako jami'an nata.

INEC ta rubuta cewa:

"Abin da ke faruwa a karamar hukumar Brass.

"Hukumar na sa ido sosai kan abin da ke faruwa a karamar hukumar Brass ta Bayelsa inda aka tsare jami'an mu.

Kara karanta wannan

INEC ta dage tattara sakamakon zaben gwamnan Bayelsa, cikakken bayani ya bayyana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wannan kawo cikas ne ga zabe mai inganci. Muna kira ga jami'an tsaro su yi gaggawan ganin an sako su."

Hakan na zuwa ne bauan kwamishinoni da mambobin majalisar jihar Bayelsa sun mamaye ofishin INEC suna cewa ba a yi zabe ba a Bassambiri da Nembe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel