Ana Ta Murna Yayin Da Akpabio Ya Rantsar Da Sanatan PDP na 2 Cikin kwana 7

Ana Ta Murna Yayin Da Akpabio Ya Rantsar Da Sanatan PDP na 2 Cikin kwana 7

  • Godswill Akpabio, shugaban majalisar dattawa, ya rantsar da Natasha Akpoti-Uduaghan daga Kogi ta Tsakiya a matsayin sanatan PDP na biyu a majalisar
  • A makon da ta gabata, Akpabio ya rantsar da Sanata Amos Yohanna daga Adamawa ta Arewa bayan fafatawarsa da tsohon Sanata Elisha Abbo
  • Akpoti-Uduaghan da Yohanna sun dauki lokaci mai tsawo suna fafatawa da abokan hamayyarsu daga APC kafin suka samu nasarar zama sanatocin Najeriya

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

FCT, Abuja - Godswill Akpabio, Shugaban Majalisar Dattawa ya rantsar da Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya bayan fafatawa a kotu na lokaci mai tsawo.

Akpoti-Uduaghan ita ce sanatan jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta biyu wacce Akpabio ya rantsar cikin mako daya. Na farkon shine Amos Yohanna, daga Adamawa ta Arewa.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan zaben sanatan PDP, LP a Arewa, an bayyana mai nasara

An rantsar da Akpoti matsayin sanata
Natasha Akpoti ta yi rantsuwar kama aiki a matsayin sanata na Kogi ta Tsakiya. Hoto: @NatashaAkpoti
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan yin rantsuwar, Akpabio ya mika wa sabuwar sanatan kwafi na dokokin majalisar ta dattawa, rahoton Daily Trust.

Daga bisani an mata jagora zuwa wurin zamanta bayan ta gama gaisawa da takwarorinta, Vanguard ta rahoto.

Yadda sabbin sanatocin PDP 2 suka tsinci kansu a Majalisa

Sabbin sanatocin biyu sun tsinci kansu a majalisa ne bayan galaba kan abokan hamayarsu daga jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Elisha Abbo da Abubakar Ohere, daga jihohin Adamawa da Kogi.

Bayan rantsar da Akpoti-Uduaghan, adadin sanatocin PDP ya karu da biyu yayin da na APC ya ragu da biyu. Wannan nasara ce ga babban jam'iyyar adawar a majalisar dattawa.

Kotun daukaka kara da ke Abuja, a ranar Litinin, ta jadada nasarar Natasha Akpoti-Uduaghan na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a matsayin sanata na Kogi ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Nasarar Tinubu a Kotun Koli: APC ta aikawa Atiku, Peter Obi sakon gaggawa

Kotun daukaka karar ta yi watsi da karar da Sanata Abubakar Ohere ya shigar kan cewa ba ta da inganci.

Tunda farko a Satumba, Kotun Sauraron Karar Zaben Jihar Kogi da ke zamanta a Lokoja ta soke nasarar Ohere na jam'iyyar All Progressives Congress, APC.

Daga bisani kotun ta ayyana Akpoti-Uduaghan ce ainihin wacce ta yi nasara a zaben sanatan.

Yan NNPP da dama sun koma PDP a Jihar Yobe

A wani rahoton, kun ji cewa wasu yan jam'iyyar NNPP a jihar Yobe sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP.

Tsohon sakataren NNPP a Arewa maso Gabas, Dr Babayo Liman ne ya sanar da hakan yayin tattaunawa da manema labarai a Damaturu, ranar Talata, 24 ga watan Janairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel