Daga Yin Barazanar Tsige Gwamna, Majalisar Dokoki ta Kama da Wuta Cikin Dare a Ribas

Daga Yin Barazanar Tsige Gwamna, Majalisar Dokoki ta Kama da Wuta Cikin Dare a Ribas

  • Ana zaune kwatsam aka ji wuta ta kama ci a majalisar dokokin jihar Ribas, an ji karar fashewar wani abu a jiya
  • Kafin gobarar ta shiga wasu sassan majalisar, jami’an tsaro da ma’aikata sun yi nasarar kashe ta tun a cikin daren
  • ‘Yan jarida sun yi bakin kokari wajen samun SP Grace Iringe Koko ta waya, ba a iya tuntubar Kakakin ‘yan sandar ba

M. Malumfashi ya yi shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Rivers - Wani bangare na majalisar dokokin jihar Ribas ya kama da wuta, zuwa yanzu ba a san musababbin wannan gobara ba.

Rahotanni daga Daily Trust da sauran gidajen jaridu sun ce hakan ya faru ne sakamakon rade-radin shirin tsige gwamnan jihar.

Wasu su na cewa akwai yunkurin tunbuke Mai girma Similanayi Fubara wanda watansa biyar rak da karbar mulkin jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Maganar tsige Gwamnan Ribas ta yi nisa, an sauke masoyinsa daga kujerar Majalisa

Ribas
Wuta ta kama Majalisar jihar Ribas Hoto: Inside Rivers State House of Assembly
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gobara ta barke a majalisar Ribas

Majiyoyi sun ce wasu miyagu sun samu shiga cikin majalisar cikin dare a ranar Lahadin nan, daga nan su ka cinna masa wuta.

Jami’an sun yi namijin kokari wajen hana wutan ci a sauran bangarorin majalisar, hakan ya takaita barnar da wutar ta yi wa ginin.

A lokacin an nemi Kakakin Kwamishinan ‘yan sandan Ribas domin jin ta bakinta, ba a iya samun SP Grace Iringe Koko ta salula ba.

Zuwa yanzu an kara baza jami’an tsaro a majalisar jihar yayin da ‘yan kwana-kwana su ka yi kokarin kawo karshen wannan gobara.

'Yan sanda sun zagaye majalisa

The Nation ta ce an ji wani kara da kimanin karfe 8:00 na dare a titin Moscow a garin Fatakwal, inda majalisar dokoki na jihar ta ke.

An zagaye wurin da motoci 17 na ‘yan sanda da tankar yaki domin a takaita lamarin.

Kara karanta wannan

Kowa ya tuna bara bai ji dadin bana ba, tsohon rasiti ya nuna yadda aka biya N340 kudin makaranta

Har zuwa yanzu jami’an ‘yan sanda ba su ce komai ba, duk da sun yi namijin kokari wajen rage barnar da wutan za ta yi a majalisar jihar.

Fubara ya karbi mulki ne daga hannun Nyesom Wike wanda ya zama minista.

Harin 'yan ta'dda a jihar Kaduna

Ana shirin yin sallar magriba kwanaki ‘yan ta’adda su ka duro kauyen Birnin Gwari, an ji labari mata da kananan yara sun bar gidajensu.

‘Yan ta’addan sun kashe mutane kuma sun shiga wani gari dabam, sun hallaka wani malami tare da dauke matarsa a yankin jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel