Birnin Gwari: An Sake Rasa Rayuka Yayin da ‘Yan Bindiga Su Ka Kai Hari a Kaduna
- A wasu hare-hare da aka kai daf-da-daf a karamar hukumar Birnin Gwari, an kashe mutane akalla hudu a jihar Kaduna
- Wani mazaunin garin na Birnin Gwari inda ‘yan bindiga su ka addaba, ya zanta da Legit a game da abin da ya wakana
- Baya ga wadanda aka hallaka, ‘yan ta’addan sun yi nasarar dauke wasu mutane tare da raba jama’a da gidajensu a jiya
Kaduna - A yammacin ranar Talata, 24 ga watan Oktoba 2023, mu ka samu labarin hari da ‘yan bindiga su ka kai a kauyukan jihar Kaduna.
Legit ta zanta da wani mazaunin karamar hukumar Birnin Gwari wanda ya tabbatar da miyagu sun aukawa wani kauye da ake kira Bagoma.
A sakamakon harin da aka kai, an tabbatar da mutuwar mutane uku, sannan Bayin Allah da-dama musamman 'yan yara sun bar gidajensu.
'Yan bindiga sun kai hari a Birnin Gwari
"Bayan magriba barayin nan sun shigo har Bagoma, akwai wani sabon gidan mai da ake kira KBY, nan su ka zo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kafin ka ce kobo kawai sai su ka fara harbi, yanzu ga mutane ne nan (‘yan yara da mata) duk sun baro yankin.
- Majiya
Majiyarmu ta shaida mana dakarun sojoji sun yi kokari wajen hallara zuwa wurin, kuma sun yi nasarar fatattakar wadannan miyagun mutane.
Kauyen Bagoma zuwa asalin garin Birnin Gwari tafiya ce da ba ta kai kilomita biyu ba. Lamarin yankin nan ya yi muni tun ba yau ba.
Sojoji sun fatattaki 'Yan bindiga
Daga baya labari ya zo mana wannan karo ma sojoji sun isa domin daga Bagoma zuwa Birnin Gwari ba zai kai tsawon kilomita daya ba.
Da mu ka zanta da shi a yau ta wayar salula, ya ce baya ga Bagoma da aka hallaka mutum uku, an shiga cikin kauyen Shekarau a jiyan.
An kashe 1, an dauke mutane 3 a Kaduna
A wannan kauye da ke kan hanyar zuwa jihar Neja, ana zargin wadannan ‘yan ta’adda sun kashe wani magidanci a yammacin Talata.
"Sun kashe wani magidanci a Shekarau, kuma sun auke matarsa da wasu mutum biyu."
- Majiya
Aminiya ta tabbatar da an hallaka limami da mamu a cikin masallaci kuma an yi awon gaba da wata matar aure da wasu 'yanuwanta biyu.
'Yan Asaru sun shigo Birnin Gwari
Labarin da mu ka samu a farkon makon nan shi ne Sojojin kungiyar Ansaru sun fara bayyana karara a yankin gabashin garin Birnin gwari
‘Yan ta’addan su na ta fadada ayyukansu na kiran al’umma domin samun magoya-baya, yanzu abin ya kai su na neman a ba su wurin zama.
Asali: Legit.ng