Ogun: DSS Ta Kama Dan Majalisar PDP Bisa Zargin Hannu a Kashe-Kashe

Ogun: DSS Ta Kama Dan Majalisar PDP Bisa Zargin Hannu a Kashe-Kashe

  • Hukumar DSS ta kama mamban majalisar dokokin jihar Ogun da wasu mutum 5 bisa zargin hannu a kashe rayuka sama da 20 a Sagamu
  • Jami'an tsaron farin kaya suna zargin ɗan majalisar na jam'iyyar PDP da hannu a rura wutar rikicin ƙungiyoyin asiri
  • Jam'iyyar PDP ta tabbatar da kama ɗan majalisar, amma ta nuna rashin jin daɗinta da matakin DSS

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ogun - Hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta damƙe ɗan majalisar dokokin jihar da wasu mutane biyar bisa zargin hannu a kashe-kashen rayuka a jihar Ogun.

Jami'an DSS sun kama waɗanda ake zargin ne bisa zargin hannu a kashe rayukan mutane sama da 20 a rikicin ƙungiyoyin asirin da ya afku a Sagamu.

Jami'an hukumar tsaron farin kaya DSS.
Ogun: DSS Ta Kama Dan Majalisar PDP Bisa Zargin Hannu a Kashe-Kashe Hoto: dailytrust

Wakilin Daily Trust ya tattaro cewa ɗan majalisar mai suna, Damilare Bello, shi ne mamba mai wakiltar mazaɓar Sagamu a majalisar dokokin jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Akpabio Na Cikin Matsala Yayin Da Shirin Tsige Shi Ke Kara Karfi, Bayanai Sun Fito

Hukumar DSS ta kama Honorabul Bello tare da Debbo Animashaun, Bamidele Saheed, Ismaila Onitire, Adewale Otesanya da kuma Tobi Owoade.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An kuma tattaro cewa an kama dan majalisar wanda aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP bisa zarginsa da hannu a rura wutar rikicin.

PDP ta yi Allah wadai da kama Honorabul Bello

Jam’iyyar PDP ta tabbatar da cewa jami'an DSS sun cafke Bello a cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai, Akinloye Bankole, ya fitar a Abeokuta.

Sai dai PDP ta yi Allah wadai da kama ɗan majalisar, inda ta ce:

"Duk da bamu adawa da matakin DSS ko wata hukumar tsaro na gudanar da bincike kan kashe-kashen Sagamu wanda ake zargin an kashe sama da mutane 25, muna ganin babu kwarewa da gaskiya a binciken da aka yi."

Haka nan kuma jam'iyyar ta ce babu wani makami ko wani abu na aikata laifi da aka samu a gidan Bello, An shafa masa kashin kaji ne domin ɓata masa suna a idon jama'a, Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe Ta Tsige 'Yan Majalisar Wakilan Tarayya 25 Da Sanatoci 5 Na Jam'iyyun APC, PDP, LP da NNPP

Tashin Hankali Yayin da Aka Kashe Sojoji da 'Yan Sanda da Yawa a Jihar Imo

A wani rahoton na daban Yan bindiga sun yi wa tawagar jami'an Soji, 'Yan sanda da Sibil defens kwantan ɓauna, sun halaka aƙalla 8 a jihar Imo.

Rahotanni daga mazauna yankin sun nuna cewa maharan sun ƙone jami'an tsaron har lahira a cikin motoci guda biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel