Tinubu Ya Nada Dan Mashood Abiola Mukamin Hadimin A Ayyuka Na Musamman

Tinubu Ya Nada Dan Mashood Abiola Mukamin Hadimin A Ayyuka Na Musamman

  • Shugaba Bola Tinubu ya nada dan marigayi Mashood Abiola (MKO) hadiminsa a bangaren ayyuka na musamman
  • Wanda aka nada mukamin, Jamiu Abiola ya kammala karatun digiri a jami'ar birnin New York da ke Amurka
  • Tinubu ya tura wasikar nadin ne ga Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume kafin tafiyarsa Amurka

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada Jamiu Abiola mukamin hadiminsa a bangaren ayyuka na musamman.

Jamiu Abiola ya kasance dan marigayi Mashood Abiola da aka fi sani da MKO wanda ya lashe zaben shugaban kasa a ranar 12 ga watan Yuni a shekarar 1993, Legit ta tattaro.

Tinubu ya nada dan Abiola mukamin hadiminsa
Tinubu ya sabon nadin mukami a gwamnatinsa. Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Jamiu Abiola.
Asali: Facebook

Yaushe Tinubu ya nada dan Abiola mukamin?

Tinubu ya tabbatar da nadin Jamiu Abiola ne a wata wasika da ya tura wa Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume kafin tafiya taron Majalisar Dinkin Duniya a Amurka.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Rundunar 'Yan Sanda A Kano Ta Yi Garambawul A Dokar Hana Fita Da Ta Kafa, Bayanai Sun Fito

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An bayyana wannan sanarwa ta mukamin Jamiu ne a yau Alhamis 21 ga watan Satumba a birnin Tarayya, Abuja.

Jamiu Abiola ya kammala digiri dinsa a jami'ar birnin New York da ke kasar Amurka, THISDAY ta tattaro.

A wani ofishi Tinubu ya tura dan Abiola?

Tinubu ya tura Abiola zuwa ofishin mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima don ta ya su cika alkawuran da su ka yi wa 'yan Najeriya yayin yakin neman zabe.

Rahotanni sun tabbatar cewa an nada Abiola wannan mukami ne son sakawa mahaifinsa ganin irin gudummawar da ya bayar a siyasar Najeriya.

Sanarwar ta ce:

"Ina mai sanar da kai cewa, mai girma shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada ka mukamin hadiminsa a bangaren ayyuka na musamman (Ofishin mataimakinsa)."

Tinubu ya nada yaron El-Rufai mukami a CBN

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa Sun Yi Martani Kan Nadin Hakeem Baba-Ahmed Mukami, Sun Tura Sako Ga Tinubu

A wani labarin, Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada Muhammad Sani Dattijo a matsayin mataimakin gwamnan babban bankin CBN.

Dattijo ya taba rike tsohon kwamishinan Kasafi da Tsare-tsare a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai.

Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Tinubu ya nada mataimakan gwamna babban bankin CBN har mutum guda hudu a lokaci guda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel