Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Likita Ya Fadi Matacce Bayan Shafe Awanni 72 Yana Aiki a LUTH

Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Likita Ya Fadi Matacce Bayan Shafe Awanni 72 Yana Aiki a LUTH

  • Wani abun bakin ciki ya samu ma'aikatan lafiya a Lagas yayin da Dr Umoh Michael ya yanke ciki ya fadi matacce a coci
  • An rahoto cewa Micheal ya shafe tsawon awanni 72 a bangaren tiyata da ke asibitin koyarwa na jihar Lagas (LUTH)
  • Biyo bayan faruwar al'amarin, kungiyar Likitoci ta yi kira ga a sake duba yanayin lokutan aikinsu

Idi-Araba, Jihar Lagas - Wani likita mai suna Dr Umoh Michael, ya yanke ciki ya mutu a coci bayan ya shafe tsawon awanni 72 a bangaren tiyata na asibitin koyarwa na jihar Lagas (LUTH).

Likitoci karkashin kungiyar likitoci na kasa (ARD), reshen LUTH ne suka bayyana hakan a cikin wata wasika zuwa ga babban daraktan kula da lafiya na LUTH, Farfesa Wasiu Lanre Adeyemo, rahoton Guardian.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Yaron Da Hanjinsa Suka Bace Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Likita ya yanke jiki ya fadi matacce a LUTH
Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Likita Ya Fadi Matacce Bayan Shafe Awanni 72 Yana Aiki a LUTH Hoto: Comrd Lawal Mustafa AbdulRaheem
Asali: Facebook

Yadda likita ya yanke jiki ya fadi, ya mutu bayan aiki na tsawon awanni 72

An yi zargin cewa Michael ya rasu ne a ranar 17 ga watan Satumba bayan ya dawo gida daga aiki da misalin karfe 3:00 na tsakar dare.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya isa gida a safiyar ranar Lahadi don zuwa coci sannan ya yanke jiki ya fadi a wajen bautar, a cocin United Evangelical da misalin 11:00 na safe.

Kamar yadda wasikar ta bayyana, abokin zaman marigayin, ya ce da kyar Dr Michael yake kwana a dakinsu a makon da ya wuce saboda yana kan amsa kira kusan kodayaushe.

"Muna da kalubale da dama a nan tunda muka fara aiki a nan kuma babban kalubalen shine yadda muke fuskantar cin zarafi daga manyanmu, yawan kira-kiraye masu cike da damuwa ba tare da hutu a tsakani ba, babu abinci kuma babu muhalli mai kyau."

Kara karanta wannan

Da gaske sojoji sun kwace mulki a kasar Kongo? Mun binciko muku gaskiyar batu

Kungiyar likitoci ta nemi a dunga duba lafiyan jami'an lafiya

Likitocin sun ce imma a dunga barin jami'an lafiya suna yin aiki na rabin rana ko kuma a bari su zo aiki da rana idan suka yi aikin dare.

Sun kara da cewar bai kamata a bar likitoci suna aiki na tsawon awanni 48 a mike ba.

Sun kuma nemi cewa dole a wajabta duba lafiyar likitoci da suka shiga aikin sabo-sabo a kyauta ko kuma a dunga yi masu sauki.

Asibitin LUTH ya karyata cewa likitoci na aiki tsawon awanni 72

Sai dai kuma, jami'ar hulda da jama'a na asibitin LUTH, Omolola Fakeye, ta yi watsi da ikirarin cewa likitoci na aiki na tsawon awanni 72 a jere.

"Zan duba rahoton lafiya na abun da ya faru saboda babu wanda zai iya cewa wani abu, amma rahoton lafiya zai nuna mana ainahin abun da ya faru."

“Ban mutu ba lokacin da suka binne ni”: Wani mutum ya ga mawaki Mohbad a mafarki

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Ta Dauki Matakin Kawo Karshen Yajin Aiki, Ta Tura Sako Ga Kungiyar NLC

A wani labari na daban, wani matashi dan Najeriya ya jaddada cewar marigayi mawakin nan na Najeriya, Mohbad bai mutu ba a lokacin da aka binne shi a harabar gidan mahaifinsa.

Matashin wanda ya yi ikirarin cewa ya yi mafarki, ya ce mawakin ya bayyana abun da ya yi sanadiyar mutuwarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel