Peter Obi Ya Daukaka Kara Zuwa Kotun Koli Don Kalubalantar Zaben Tinubu

Peter Obi Ya Daukaka Kara Zuwa Kotun Koli Don Kalubalantar Zaben Tinubu

  • Peter Obi, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar, Labour ya daukaka kara kan zaben shugaban kasa
  • Obi ya daukaka karar ce don kalubalantar hukuncin kotun kararrakin zabe da ta yi hukunci a farkon wannan wata
  • A yayin hukuncin kotun, an tabbatar da Bola Tinubu na jam'iyyar APC a matsayin zababben shugaban kasa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyar Labour, Peter Obi ya daukaka kara zuwa kotun koli don kalubalantar zaben shugaban kasa.

Peter Obi da jam'iyyarsa ta Labour sun daukaka karar ce don kalubalantar zaben da ta ayyana Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa.

Peter Obi ya daukaka kara kan zaben Tinubu
Peter Obi ya bi sahun Atiku na daukaka kara kan zaben Tinubu. Hoto: Peter Obi, Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Twitter

Meye Peter Obi ke kara kan zaben Tinubu?

Kotun a farkon wannan wata ta tabbatar da Bola Tinubu na jam'iyyar APC a matsayin halastaccen shugaban kasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Kotun Zabe Ta Rusa Nasarar Kakakin Majalisar Jihar Arewa, Ta Bai Wa PDP Nasara

Obi ya daukaka karar ce a yau Talata 19 ga watan Satumba a birnin Tarayya Abuja, cewar TheCable.

Obi a cikin korafe-korafen da ya gabatar ya bayyana cewa kotun ba ta yi masa adalci ba yayin yanke hukuncin da ta yi a farkon wannan watan da mu ke ciki.

Meye korafin Peter Obi kan zaben Tinubu?

Ya ce hukuncin kotun karkashin jagorancin Mai Shari'a Haruna Tsammani akwai kuskure da kuma rashin yi masa adalci yadda ta kori karar da cewa bai ba da gamsassun hujjojin inda aringizon kuri'un su ka faru ba.

Ya akara da cewa kotun ta tauye masa hakkin ba shi damar gabatar da shaidu inda ya ce an yi fatali da shaidunsa da cewa ba su da karfi, cewar Vanguard.

Har ila yau, Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP shi ma a yau Talata 19 ga watan Satumba ya daukaka kara a kotun koli.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Shirya Daukar Matakin Kwace Mulki A Hannun Tinubu, Ya Bayyana Hujjoji

Atiku da Peter Obi na kalubalantar sahihancin zaben Bola Tinubu na jam'iyyar APC a matsayin shugaban kasa.

Atiku ya daukaka kara kotun koli don kan zaben Tinubu

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya daukaka kara don kalubalantar zaben Bola Tinubu.

A ranar 6 ga watan Satumba ne kotun sauraran kararrakin zabe a Abuja ta yi fatali da karar da ya shigar a kotun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel