Jamila Bio: Abubuwa 20 a Kan Macen da Tinubu Ya Zaba Ta Zama Ministar Matasa

Jamila Bio: Abubuwa 20 a Kan Macen da Tinubu Ya Zaba Ta Zama Ministar Matasa

  • Jamila Ibrahim Bio ta kama hanyar kafa tarihi tun da Bola Tinubu ya zabi ta zama Ministarsa
  • Wannan likita mai shekara 37 za ta sama cikin ‘yan autan ministocin da su ka taba zama a FEC
  • Dakta Jamila Bio ta bi sahun mahaifinta wanda ya kasance minista lokacin gwamnatin PDP a kasar nan

FCT, Abuja - Da zarar an tantance Dakta Jamila Ibrahim Bio a Majalisar Dattawa, za ta zama sabuwar ministar harkokin matasa a Najeriya.

Abin da rahoton nan ya kunsa shi ne bayani kan tarihin rayuwa da siyasar Jamila Ibrahim Bio mai shirin bin tafarkin mahaifinta.

Minista
Dr. Jamila Ibrahim Bio za ta zama Minista Hoto: @DrJamilaIbrahim
Asali: Twitter

Wacece Dr. Jamila Bio

Fadar shugaban kasa ta fitar da bayani a game da Dr. Jamila Bio:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Shara ta kare a Kano, Abba Gida-Gida ya dauki ma'aikatan tsaftace birni mutum 4500

1. An haifi Dr. Jamila Bio a Fabrairun 1986, yanzu haka ta na da shekara 37 a duniya.

2. Mahaifinta shi ne Ibrahim Isa Bio wanda ya taba zama minista kuma ya yi aiki a Majalisar Dokokin Jihar Kwara da majalisar wakilan kasa.

3. Ministar goben kwararriyar likita ce, ta samu shaidar MBBS a Jami’ar Unilorin a 2010.

4. Baya ga haka, ta na da satifiket a fannin likitanci a wata jami’ar da ke birnin Washington, Amurka.

5. Tsakanin 1996 da 2002, Bio ta yi karatun sakandare a Makarantar Gwamnatin Mata da Bwari.

6. A 1996 ne ta samu shaidar firamare a wata makaranta a garin New Bussa a Jihar Neja.

7. ‘Yar siyasar ta yi aiki da Majalisar Dinkin Duniya kuma hadimar gwamna a fannin SDG.

8. Kafin yanzu, ta kasance mai ba Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq shawara kan lafiya.

9. Baya ga haka, ta taka rawar gani a kwamitin farfado da yankin Arewa maso gabas.

10. Tun tuni Jamila Bio ta ke fafutuka domin ganin ana damawa da matasa da mata a mulki.

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Ɗalibar Jami'ar Tarayya Ta Mutu a Hanyar Zuwa Kasuwa

11. Kyaututtukan da ta samu sun hada da na gwamnan Kwara, kungiyoyin NANS da NAKSS.

12. A shekarun baya ta yi magana a zauren kungiyar AU da kuma Majalisar Dinkin Duniya.

13. Musamman Jamila Bio ta jagoranci wata tafiya domin yaki da yunwa a jiharta a 2020.

14. Sannan ta hada-kai da Gwamnatin Tarayya duk a 2020 domin samar da ruwa mai tsabta.

15. Daga cikin abubuwan da ta ke sha’awa akwai wasa da doki da polo.

16. A Mayun 2020 aka nada ta a matsayin jagorarar AUDA-NEPAD ta kasashen Afrika.

17. Yanzu haka ta na cikin darektocin kungiyar Emirates Equestrian Club a birnin Ilorin.

18. A bangaren siyasa, ta yi aiki da kwamitocin yakin zaben shugaban kasa ta PCC a 2023.

19. Har ta kafa gidauniya mai suna Jamila Bio Ibrahim domin horar da matasa a Najeriya.

20. Idan ta shiga ofis, za ta zama macen farko da ta zama ministar harkokin matasa a Najeriya.

Tinubu zai nada Gwamnan CBN

Kara karanta wannan

Gwamnan CBN: Abubuwa 11 da Ya Dace Mutane Su Sani Kan Wanda Tinubu Ya Dauko

Idan Majalisar Dattawa ta tantance Dakta Olayemi Micheal Cardoso, zai zama sabon Gwamnan CBN, kun ji labarin shi ne zai canji Godwin Emefiele.

Kamar Ministan Kudi da sabon shugaban FIRS, Cardoso ya fito ne daga yankin Kudu maso Yamma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel