Oyo: Kotu Ta Umarci INEC Ta Sake Zabe a Mazabar Saki Ta Yamma

Oyo: Kotu Ta Umarci INEC Ta Sake Zabe a Mazabar Saki Ta Yamma

  • Kotu ta soke zaɓen ɗan majalisar jam'iyyar APC mai wakiltar mazaɓar Saki ta Yamma a majalisar dokokin jihar Oyo
  • Hon. Shittu Ibrahim Aremu ya rasa kujerarsa ne bayam ɗan takarar jam'iyyar PPDP ya ƙalubalanci nasarar da ya samu a kotu
  • Kotun ta kuma umarci hukumar zaɓe ta INEC da ta sake gudanar da sabon zaɓe a cikin 90 masu zuwa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Oyo - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisun tarayya mai zamanta a Ibadan na jihar Oyo, ta bayar da umarnin sake zaɓe a mazaɓar Saki ta Yamma a ta majalisar dokokin jihar.

Jaridar PM News ta rahoto cewa alƙalan kotun guda uku su ne suka sanar da wannan hukuncin a ranar Alhamis, 14 ga watan Satumban 2023.

Kotu ta umarci a sake zabe a mazabar Saki ta Yamma
Kotu ta kwace kujerar Hon. Shittu Ibrahim Hoto: Hon. Shittu Ibrahim Aremu
Asali: Facebook

Tun da farko hukumar zaɓe ta INEC ta bayyana Mista Shittu Ibrahim na jam'iyyar All Peoples Congress (APC) a matsayin wanda ya lashe zaɓen na ranar 18 ga watan Maris.

Hukumar ta bayyana cewa Ibrahim ya samu ƙuri'u 13,692 inda ya yi nasara akan ɗan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Mista Julius Okedoyin, wanda ya samu ƙuri'u 13,422 a zaɓen.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Meyasa kotu ta ce a sake zaɓe?

Da yake sanar hukuncin kotun, mai shari'a Jubril Anaja, ya tabbatar da cewa ƙarar ta cancanta kuma masu shigar da ƙarar sun kawo ƙwararan hujjoji domin kare ƙarar da suka shigar.

Anaja ya bayyana cewa soke sakamakon zaɓen mazaɓa ta 6 da 7 da mazaɓa ta 11 da 19 na gundumar, inda aka karɓi katin zaɓe 1,285, na iya yin tasiri matuƙa ga sakamakon zaɓen.

Kotun ta yi nuni da cewa, yayin da wanda aka bayyana ya lashe zaɓen ya yi nasara kan mai shigar da ƙarar da kuri’u 270, adadin waɗanda aka hana su zabe ya haura 1,000.

Ta yi hukuncin cewa waɗanda aka hana zaɓen a mazaɓun da abin ya shafa ka iya sauya sakamakon zaɓen da an ba su damar yin zaɓe.

Kotun ta jingine shaidar lashe zaɓe da INEC ta ba Ibrahim, sannan ta umarci hukumar ta sake gudanar da zaɓe a mazaɓun da abin ya shafa cikin kwana 90.

Kotu Ta Soke Zaben Yar Majalisar PDP

A wani labarin kuma, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisun tarayya ta soke zaɓen ƴar majalisar wakilai ta jam'iyyar PDP mai wakiltar Langtang ta Arewa/Langtang ta Kudu.

Kotun ta bayyana ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress, Vincent Bulus, a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaɓen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel